Shugaban riƙon ƙwarya na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Sanata David Mark, ya bayyana jam’iyyar a matsayin wata hanya da za a bi don cimma haɗin kan Arewa, da cigaba da kawo ci gaban yankin. Ya bayyana haka ne a jawabin buɗe taro na uku na babbar ganawar ƙungiyar tuntuɓa a siyasa (NPCG) ta Arewa, a Abuja.
Taron wanda ya gudana bayan bayyana ADC a matsayin sabon dandalin siyasa ga wasu fitattun ‘yan adawa gabanin zaɓen 2027, ya nemi hanyoyin da za a bi wajen haɗa kan al’ummar Arewa. A taro na baya, ƙungiyar NPCG ƙarƙashin jagorancin tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ta bukaci a gaggauta bayyana wata sabuwar jam’iyya domin kare muradun yankin.
- ADC Ga Tinubu: Ina Wutar Lantarki Ta Awa 24 Da Ka Yi Wa ‘Yan Nijeriya Alkawari?
- Dele Momodu Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP Zuwa ADC
A cewar Sanata Mark, Arewa na cikin wani hali mai sosa rai, yana mai jaddada cewa ‘yan Arewa su ne za su iya magance matsalolin da ke damun su. Ya buƙaci a guji maganganu masu tayar da fitina da siyasar rarrabuwa, tare da mayar da hankali kan muhimman ayyuka kamar ilimi, da kiwon lafiya da ababen more rayuwa.
Sanata Mark ya bayyana cewa duk da albarkatun ƙasa, arziƙin noma, da yawan al’adu, Arewa na fama da matsaloli da suka haɗa da rashin tsaro, talauci, rikice-rikicen ƙabilanci da na addini, da kuma gazawar ci gaban tattalin arziki da siyasa. Ya bayyana yadda rashin tsaro ke hana masu zuba jari shiga yankin, wanda ke ƙara ƙarfafa fatara da laifuka.
Ya koka kan yadda ake amfani da ƙabilanci da addini wajen haifar da rikice-rikice don biyan buƙatun wasu. Ya buƙaci al’umma su koma ga zaman lafiya da juna da suka yi fice da shi a baya, inda kalmar “Ɗan Arewa” ke bayyana duƙulalliyar halayyarsu. Mark ya jaddada cewa ADC za ta kawo bambanci, domin a wajensu siyasa ibada ce, ba hanya ta yaudara ba. Ya ƙara da cewa dole ne Arewa ta farka daga wannan yanayi, domin a da yankin ne mafi aminci a Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp