Tsohon mataimakin kocin tawagar Super Eagles ta Nijeriya, Salisu Yusuf ya ajiye aikinsa na horar da kungiyar Nasarawa United wacce ya karbi aikin horar da ita a watannin karshen kakar wasan da ta gabata, kocin mai shekaru 63 ya taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa kungiyar tsallakawa zuwa matakin kusa da na karshe na gasar cin kofin shugaban kasa.
A halin yanzu, ya shilla zuwa Cotonou babban birnin kasar Benin domin kammala saka hannun akan yarjejeniya da wata babbar kungiya a kasar, kafin karbar tayin daga kungiyar ta Benin, Yusuf ya samu kira daga tsohon kulob dinsa na Kano Pillars, wannan dai shi ne karon farko da zai jagoranci wata kungiya a wajen Nijeriya.
Yusuf ya jagoranci kungiyoyin kwallon kafa da dama a Nijeriya da suka hada da Kano Pillars, Nasarawa United da Rangers International, ya fara aikin horarwa a shekarar 2002 a matsayin babban kocin kungiyar kwallon kafa ta Nasarawa United kafin ya koma Lobi Stars a matsayin mataimakin koci inda ya taimaka musu su suka lashe kogin FA na Nijeriya, a shekarar 2008 ya taimakawa Kano Pillars wajen lashe kofin Firimiya.
A shekara ta 2009, hukumar Kwallon Kafa ta Nijeriya ta dauki Yusuf aiki a matsayin mataimakin koci ga Samson Siasia wanda ke rike da mukamin babban kocin tawagar kwallon kafa ta Nijeriya, Yusuf har yanzu yana aiki da Siasia, ya taimakawa Pillars samun gurbin shiga gasar cin kofin CAF, a shekarar 2012 ya koma Enyimba inda ya maye gurbin Austin Eguavoen a matsayin koci kuma ya taimaka masu wajen lashe kofin gasar Federation Cup na shekarar 2013.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp