Jami’an tsaro sun kama wani wakilin jam’iyya da kuɗi fiye da miliyan ₦25.9, wanda ake zargin za a yi amfani da shi ne don sayen masu kaɗa kuri’a a zaɓen cike gurbi da za a gudanar ranar Asabar a Kaduna.
Shehu Aliyu Patangi, wanda aka kama a wani shahararren Otel a Titin Turunku da misalin ƙarfe 3:30 na safiyar Asabar, ya bayyana wa jami’an tsaro cewa kuɗin an tanade shi ne don bayar da cin hanci ga masu kaɗa ƙuri’a a Chikun/Kajuru. An kwato dukkan kuɗin daga hannunsa.
- An Taƙaita Zirga-Zirga A Ƙananan Hukumomi 4 Kafin Zaben Cike Gurbi A Kano
- INEC Ta Gargaɗi Ƴan Siyasa Kan Azarɓaɓin Yaƙin Neman Zaɓen 2027
Kwamishinan Ƴansanda na Kaduna, CP Rabiu Muhammad, ya yaba da haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro, ya kuma yi gargaɗi ga duk wani mai ƙoƙarin kawo tarnaƙi ko cikas a zaɓen, cewa zai fuskanci hukunci mai tsanani.
Hukumomin tsaro sun yi kira ga al’umma da su fito lafiya su yi amfani da haƙƙinsu na kaɗa ƙuri’a ba tare da tsoro ko tayar da hankali ba, yayin da aka tabbatar da tsaro a duk wuraren da ake sa ran rikici.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp