Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya sanar da cewa jami’an tsaro sun kama manyan shugabannin ƙungiyar ‘yan ta’adda ta Ansaru bayan watanni ana nemansu ruwa a jallo.
Waɗanda aka kama sun haɗa da Mahmud Muhammad Usman, wanda aka fi sani da Abu Baraa, wanda shi ne shugaban ƙungiyar, da kuma mataimakinsa Mahmud al-Nigeri, wanda aka fi sani da Mallam Mamuda.
Ribadu ya ce dukkanninsu sun shafe shekaru suna cikin jerin waɗanda ake nema bisa laifin kai wa jami’an tsaro da mutane hare-hare da gine-ginen gwamnati.
A lokacin da yake jawabi a Abuja ranar Asabar, Ribadu ya bayyana wannan a matsayin babban ci gaba a yaƙi da ta’addanci a Nijeriya.
Ya ce Abu Baraa shi ne yake kiran kansa “Sarkin Ansaru” tare da sama maɓoyar ta’addanci a sassa daban-daban na ƙasar nan.
Ya kuma jagoranci sace mutane da fashi don tara kuɗaɗen da suke amfani da su wajen aikata ta’addanci.
Mataimakinsa Mamuda shi ne ke jagorantar rukunin “Mahmudawa” wanda ke aiki a kusa da Kainji National Park da ke tsakanin Jihar Neja da Kwara har zuwa Jamhuriyar Benin.
Ribadu ya ce Mamuda ya samu horo a Libya tsakanin shekarun 2013 da 2015, inda ya koyi amfani da makamai da kuma haɗa bama-bamai.
Ƙungiyar Ansaru ta fara ne a shekarar 2012 bayan ta ɓalle daga Boko Haram.
A farko ta yi ikirarin jihadi, amma daga baya ta fara kai wa jami’an tsaro, al’umma, da kuma gine-ginen gwamnati hare-hare.
Ƙungiyar kuma tana da alaƙa da Al-Qaeda a Arewacin Afirka.
A tsawon shekaru, ana danganta ƙungiyar da manyan laifuka da suka haɗa da balle gidan yarin Kuje a 2022, harin wajen haƙar uranium a Nijar, sace injiniyan Faransa Francis Collomp a 2013, sace Alhaji Musa Umar Uba na Daura a 2019, da kuma sace Sarkin Wawa.
Ribadu ya ce har yanzu suna da alaƙa da ƙungiyoyin ta’addanci a Mali, Nijar da Burkina Faso.
Ministan Watsa Labaru, Mohammed Idris, ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su riƙa bai wa jami’an tsaro bayanai masu amfani don kawo ƙarshen ta’addanci.
Ya kuma roƙi kafafen yaɗa labarai kada su riƙa yaɗa manufar ‘yan ta’addan domin samun karɓuwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp