Aƙalla mutum takwas ne suka rasu, yayin da wasu da dama suka jikkata a harin ‘yan bindiga guda biyu da suka kai ƙananan hukumomin Kauru da Kudan a Jihar Kaduna.
A Kauru, ‘yan bindigar sun kutsa cikin Ungwan Rimi da safiyar ranar Litinin, inda suka fara harbin jama’a tare da kashe mutane.
- Gwamnati Ta Fara Aikin Gyara Na’urar Watsa Shirye-shirye Mai Gajeren Zango Ta Gidan Rediyon Muryar Nijeriya
- Hukumar NRC Ta Dakatar Da Zirga-zirgar Jiragen Kasa Na Abuja zuwa Kaduna
Shugabannin al’umma sun ce rikicin ya samo asali ne daga wani rikici a Jihar Filato wanda ya bazu zuwa Kauru.
A wani hari daban, ‘yan bindiga sun kashe mutum ɗaya sannan suka sace wani attajiri mai suna Shehu Hussein a Ungwan Fulani, a ƙaramar hukumar Kudan.
Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi tir da harin, inda ta ce hare-haren na daga cikin waɗanda da ake samu a yankunan a baya-bayan nan.
Gwamna Uba Sani ya umarci jami’an tsaro da su kamo waɗanda suka aikata laifin tare da wanzar da zaman lafiya.
Jami’ai sun ce jihar ta samu zaman lafiya sosai cikin shekaru biyu da suka gabata sakamakon Kaduna Peace Model, wanda ya rage rikice-rikice tare da sake ba da damar zuwa gonaki da kasuwanni a wuraren da aka daɗe ana fama da rikici.
Sai dai sun yi gargaɗin cewa rashin tsaro daga jihohin maƙwabta na yawan zuwa cikin Kaduna, don haka ana buƙatar gwamnatoci na jihohi su haɗa kai domin kawo ƙarshen irin waɗannan hare-hare a nan gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp