• English
  • Business News
Saturday, August 30, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Akwai Bukatar Gwamnonin Arewa Su Yi Koyi Da Jihar Legas Wajen Bunkasa Albarkatun Fatu

by Bello Hamza and Sulaiman
14 hours ago
in Rahotonni
0
Akwai Bukatar Gwamnonin Arewa Su Yi Koyi Da Jihar Legas Wajen Bunkasa Albarkatun Fatu
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Lokacin da Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Jihar Legas ya kaddamar da kamfanin fata na Mushin, wato ‘Industrial Leather Hub’ tare da hasashen samun kudaden fitarwa na shekara-shekara na Naira biliyan 387.5, hakan sai ya bayyana wani babban rashin daidaito a ci gaban Nijeriya.

 

Legas, ba ta da wani tushe na kiwo, amma ta nuna jagoranci da hangen nesa, yayin da Arewacin kasar da ke da yawan dabbobi da fatu suka gaza wajen bunkasa a fannin fata ba.

 

Wannan rubutu ya yi nazari ne kan yanayin masana’antar fata ta duniya da ta cikin gida, wanda kuma itace damar da Nijeriya ta rasa, gudunmawata a matsayin tsohon Shugaba/ Darakta Janar na NILEST, ya zama dole gwamnonin Arewa su dauki matakan gaggawa don farfado da wannan sashe.

Labarai Masu Nasaba

Ranar Hausa: Yadda Hausawa Ke Tunƙaho Da Harshensu A Faɗin Duniya

Masana Sun Gano Dalilan Da Ke Taimaka Wa Ballewar Daurarru A Gidan Yari

 

Tare da jagoranci da zuba jari, Nijeriya na iya samun fiye da Dala biliyan 4 a shekara a kudaden fitar da fata, kirkirar miliyoyin ayyukan yi, da kuma dawo da matsayin tarihi a matsayin babbar mai karfi a duniya a fannin fata.

 

Misali daga Jihar Legas

Jihar Legas kwanan nan ta kaddamar da Mushin Industrial Leather Hub, da nufin samar da kudaden fitarwa na Naira biliyan 387.5 a kowace shekara. Wannan abin ban mamaki ne, idan aka yi la’akari da cewa Legas ba ta da wani tushe a fannin kiwo. Wannan kaddamarwar tana nuni wani rashin daidaito: a yanzu dai Legas ce ke jagoranci tare da hangen nesa da tsara dabarun da ya kamata a ce jihohin Arewa ne ke kai, wadanda ke da yalwar kiwo, amma an bar su a baya. Wannan na haifar da ayar tambaya cewa: me ya sa Legas ke jagorantar masana’antar fata yayin da a ce Arewa ce Arewa ce ta yi fice akan hakan?

 

Harkar Fatu A Duniya

Masana’antar fata ta duniya tana da kimar samun fiye da Dala biliyan 400 a duk shekara, inda kasuwannin kayan kwalliya, takalma, motoci, da kayayyakin alfarma ke tafiyar da shi. Afirka na bayar da kusan kashi 30 na fata da ba a sarrafa ba na duniya amma tana bayar da kashi 6 ne kawai na fitar da fata da aka sarrafa, wanda kimarsa ta kai Dala biliyan 3.5.

 

Kasar Morocco kadai na samun fiye da Dala miliyan 500 a shekara daga fitar da fata da aka gama sarrafawa. Wani abin ban dariya shi ne shahararriyar fatar Morocco, wanda aka saba kira da ‘Morocco Leather’, an yi ta ne daga fatar akuya da asalinta daga Sakkwato take wato ‘Sokoto Red, wacce asalin ta daga Arewa Nijeriya ce.

 

Yayin da Morocco ta samu suna mai karfi a duniya, Nijeriya ta bari karfinta ya ragu, ta rasa damar..

 

Arzikin Da Ke Tattare Da Harkar Fatu A Nijeriya

Nijeriya na daya daga cikin manyan masu samar da fata daga fatar dabbobi a Afirka, inda dabbobi ke da yawa a jihohin Arewa kamar Kano, Sokoto, Katsina, Bauchi, da Borno. Wannan sashi na masana’antu yana daukar ma’aikata kusan 750,000, ciki har da sama da 500,000 a kananan masana’antar kayan karshe kamar takalma da jakunkuna. Duk da haka, fiye da kashi 90 na fatar Nijeriya ana fitar da ita ce kawai a asalinta ko kafin sarrafawa, wanda ke hana kasar samun karin kima da kudaden fitarwa mafi girma.

 

Tsofaffin gungun masana’antar fata da suka bunkasa a Kano da Sokoto sun ragu, inda fiye da masana’antar fata 40 suka rufe a cikin shekaru ashirin da suka gabata.

 

Na Kafa Gaggarumun Ginshiki A Jagorancina A NILEST

A matsayina na Shugaba/Daraktan Janar na Nigerian Institute of Leather and Science Technology (NILEST), na gane cewa fata wani muhimmin jigo ne wajen tsara manufofin bambance-bambancen tattalin arzikin Nijeriya. Na jagoranci shirye-shiryen sauyi wadanda suka kafa tubalin farfado da masana’antar.

 

Kafa sabbin Cibiyoyin Horarwa da Fadada Ilimin Fata guda 23 a fadin kasa, don tabbatar da cewa kwarewar fata da horo sun isa kowane sashe na Nijeriya.

 

Kirkirar shirye-shiryen farfado da masana’antar fatu da taswirar fasaha ga manyan gungun masana’antar Arewa.

 

Jagorancin Kwamitin Kula da Manufofin Fata da Kayayyakin Fata na Kasa, wanda ya samar da cikakkiyar manufar fata ta farko a Nijeriya.

 

Hadin gwiwa da kasashen waje, ciki har da ziyara zuwa Portugal don samun hadin gwiwa a fannin canja fasaha, horo, da samun damar kasuwa.

 

Zuba jari a bincike da ci gaba, tare da mai da hankali kan hanyoyin tanning masu tsabtace muhalli da kirkirar kayayyaki.

 

Shirye-shiryen horo da suka ba da karfi ga masu sana’a, matasa, da mata a fannin kimar fata.

 

Dalilin Nasarar Legas, Arewa Kuma Aka Yi Shiru

Legas na bunkasa ne saboda hangen nesa, kayan aiki, da shugabanci. Gwamnatinta ta jajirce wajen masana’antu, ba tare da la’akari da albarkatun kasa ba. Arewa, a dayan hannun kuma, tana ci gaba da dogaro da dabbobi ba tare da hada shi da manufofi, zuba jari, ko hangen nesa ba. Wannan gibin shugabanci shi ne ke bayyana dalilin da ya sa Legas ke kan gaba wajen fitar da fata, yayin da Arewa ke ci gaba da zama mai samar da albarkatun fatar na asali.

 

Hanyoyin Da ZA A Bunkasa Harkar Fatu A Arewa

Domin cimma burin karfafa masana’antar fata, Arewa Nijeriya dole ne ta kammala tsarin ta hanyar canzawa daga fitar da fata a asali zuwa samar da kayayyaki masu kima. Muhimman hanyoyi sun hada da:

 

a. Bukatun Manufofi:

Tilasta takunkumi kan fitar da fata a asali.

Sabunta Mahauta (abattoirs).

Karfafawa wajen farfado da masana’antar tanning da zamani.

Hada ci gaban fata cikin manufofin masana’antu na jiha.

 

b. Dabarun Zuba Jari:

Gina hadin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu wajen bunkasa masana’antar tanning da cibiyoyin masana’antu.

Jan hankalin masu zuba jari na kasashen waje tare da karfafawa ta musamman.

Hada cibiyoyin masana’antar fata da yankunan tattalin arziki na musamman (special economic zones).

 

c. Ayyukan Yi da Tasirin Al’umma:

Fadada ayyukan yi a wannan sashe zuwa miliyan 1.5–2 a cikin shekaru goma masu zuwa.

Ba da fifiko ga hadin kan matasa da mata a cikin gungun masana’antar fata.

 

d. Hasashen Fitarwa

Nijeriya na iya samun Dala biliyan 4 a fitar da fata shekara-shekara nan da 2030.

Samun isasshen lokaci: samun kashi 5 zuwa 10 na fitar da fata da aka sarrafa a duniya, wanda kimarsa ta kai Dala biliyan 20 zuwa 30.

 

Nazarin Yadda Lamarin Yake A Morroco da Sakkwato

Fatar Morocco ta zama shahararriyar alama a duniya, duk da cewa ta samo asali ne daga akuya kuma daga Jihar Sakkwato wato ‘Sokoto Red. Morocco ta gina karfi wajen nuna alama, gungun abin da ake fitarwa, da tsarin masana’antu, yayin da Nijeriya ke fitar da fata ta asali. Darasin shi ne a fili: alamar kasuwanci, manufofi, da hangen nesa ne ke kirkirar masana’antu masu karfi a duniya.

 

Shawarwari Ga Gwamnonin Arewa

Kafa cibiyoyin masana’antar fata na jiha da na masu zaman kansu, da hada su da cibiyoyin NILEST.

 

Tallafa wa hadakar masana’antar tanning da fasaha ta zamani da kuma samar da kudi.

 

Hadin gwiwa da cibiyoyin masana’antu na Legas da na kasashen waje don karfafa sarkar kimar fata.

 

Karfafa kafa Kwamitocin Kimar Fata a kowace jiha.

Karfafa zuba jari daga ‘yan kasa a waje da sashin masu zaman kansu a kayayyakin fata da aka gama sarrafawa.

 

Bukatar Samar Da Kyakyawan Shugabanci

Legas na da karancin dabbobi amma tana da hangen nesa mai yawa. Arewa na da yalwar dabbobi amma babu shugabanci. Arziki ba ya fitowa daga albarkatu kadai ba, sai daga hangen nesa, manufofi, da aiki mai manufa. Arewa ba za ta iya ci gaba da zama ‘yar kallo kawai a juyin juya halin masana’antar fata ta Nijeriya ba.

 

Ta hanyar gini kan tubalan da aka kafa a NILEST, cibiyoyi 23, tsarin farfado da masana’antar tanning, hadin gwiwar kasa da kasa, da manufofin kasa, shugabannin Arewa za su iya sanya Nijeriya ta zama mai karfin samar da fata a duniya. ‘Sokoto Red goat’, masana’antar Kano’s tannery heritage, da yalwar dabbobi a Bauchi da Maiduguri’s libestock wealth’ dole ne a yi amfani da su ba a matsayin kayan fitarwa a asali ba, har ma a matsayin kayayyakin karshe da za su samar da ayyukan yi, kudin waje, da alfahari.

 

Idan Legas na iya yin mafarki na samun kudaden fitar da fata ta Naira biliyan 387.5 ba tare da dabbobi ba, Arewa na iya cimma fiye da haka da yalwar albarkatunta, muddin ta zabi hangen nesa maimakon zamanta haka nan.

 

Farfesa Muhammad Kabir shi ne tsohon shugaban Cibiyar kimiyyar Sarrafa Fatu (NILEST) da ke Zariya. Kuma shi ne tsohon shugaban tsare-tsare na kasa na kwamitin shugaban kasa kan bunkasa fatu a Nijeriya.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

An Gabatar Da Shirin Musayar Al’adu Na “Echoes Of Peace” A Mexico

Next Post

Tottenham Ta Ɗauki Xavi Simons Daga RB Leipzig

Related

Ranar Hausa: Yadda Hausawa Ke Tunƙaho Da Harshensu A Faɗin Duniya
Rahotonni

Ranar Hausa: Yadda Hausawa Ke Tunƙaho Da Harshensu A Faɗin Duniya

4 days ago
Masana Sun Gano Dalilan Da Ke Taimaka Wa Ballewar Daurarru A Gidan Yari
Rahotonni

Masana Sun Gano Dalilan Da Ke Taimaka Wa Ballewar Daurarru A Gidan Yari

1 week ago
Dambarwar 2027 Da Kalubalen Da Ke Gaban Jam’iyyun Siyasa
Rahotonni

Dambarwar 2027 Da Kalubalen Da Ke Gaban Jam’iyyun Siyasa

2 weeks ago
Rawar Da Dakta Bello Matawalle Ke Takawa Wajen Inganta Harkokin Tsaro A Nijeriya
Rahotonni

Rawar Da Dakta Bello Matawalle Ke Takawa Wajen Inganta Harkokin Tsaro A Nijeriya

2 weeks ago
Tinubu Ya Yi Wa Arewa Kokari Fiye Da Duk Wani Shugaba A Tarihin Nijeriya -Kwamared Dauda
Rahotonni

Tinubu Ya Yi Wa Arewa Kokari Fiye Da Duk Wani Shugaba A Tarihin Nijeriya -Kwamared Dauda

2 weeks ago
Yadda Masu Bukata Ta Musamman Suka Rungumi Sabbin Dabarun Noma Domin Ciyar Da Kansu
Rahotonni

Yadda Masu Bukata Ta Musamman Suka Rungumi Sabbin Dabarun Noma Domin Ciyar Da Kansu

1 month ago
Next Post
Tottenham Ta Ɗauki Xavi Simons Daga RB Leipzig

Tottenham Ta Ɗauki Xavi Simons Daga RB Leipzig

LABARAI MASU NASABA

NDLEA Ta Kama Wani Matashi Dan Shekara 29 Da Kwayoyin Tramadol 7,000 A Kano

NDLEA Ta Kama Wani Matashi Dan Shekara 29 Da Kwayoyin Tramadol 7,000 A Kano

August 30, 2025
A Karo Na 3 Cikin Wata Guda, Jirgin Ruwa Ya Sake Kifewa A Sakkwato

A Karo Na 3 Cikin Wata Guda, Jirgin Ruwa Ya Sake Kifewa A Sakkwato

August 30, 2025
tallafi

Kudaden Ajiya Na Asusun Nijeriya Ya Karu Zuwa Dala Biliyan 41

August 30, 2025
Gwamnatin Katsina Za Ta Sayo Babura 700 da Motoci 20 Don Samar Da Tsaro

Gwamnatin Katsina Za Ta Sayo Babura 700 da Motoci 20 Don Samar Da Tsaro

August 30, 2025
ADC Ta Bukaci Tinubu Ya Kafa Dokar Ta Baci A Katsina Da Zamfara Kan Rashin Tsaro

ADC Ta Bukaci Tinubu Ya Kafa Dokar Ta Baci A Katsina Da Zamfara Kan Rashin Tsaro

August 30, 2025
A Zango Mai Zuwa Za A Fara Aikin Dala Miliyan Daya A Tashar Jirgin Ruwa Ta Legas – Dantsoho

A Zango Mai Zuwa Za A Fara Aikin Dala Miliyan Daya A Tashar Jirgin Ruwa Ta Legas – Dantsoho

August 30, 2025
Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Kara Azamar Bunkasa Da’a A Harkokin Jam’iyya

Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Kara Azamar Bunkasa Da’a A Harkokin Jam’iyya

August 29, 2025
katin zabe

INEC Ta Bayyana Damuwarta Kan Katunan Zabe 360,000 Da Ba A Karba Ba A Kano

August 29, 2025
Sin Ta Sanar Da Rukuni Na Hudu Na Abubuwa Da Wuraren Tunawa Da Yakin Kin Jinin Mamayar Dakarun Japan

Sin Ta Sanar Da Rukuni Na Hudu Na Abubuwa Da Wuraren Tunawa Da Yakin Kin Jinin Mamayar Dakarun Japan

August 29, 2025
Jam’iyyar PDP Ta Janye Daga Shiga Zaɓen Ƙananan Hukumomi A Kebbi

Shugabannin PDP Sun Shiga Dimuwa Yayin Da APC Ke Zawarcin Wasu Gwamnoninsu

August 29, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.