Jihar Sokoto ta sake fuskantar wani mummunan hatsarin jirgin ruwa, karo na uku a cikin wannan watan, inda aka tabbatar da mutuwar mutum biyu yayin da aka ceto mutane tara.
Hatsarin ya faru ne da yammacin Juma’a a kogin Jaranja da ke ƙaramar hukumar Shagari, kamar yadda Shugaban Hukumar Ruwa ta Ƙasa (NIWA) a Sokoto, Bala Bello, ya tabbatar. Ya ce hatsarin ya samo asali ne daga sakaci, da ɗaukar kaya da fasinja fiye da ƙima da kuma karya ƙa’idojin tafiya a ruwa lafiya.
- BUA Siminti Ya Ƙaddamar Da Shirin Horas Da Matasan Sakkwato
- Mutane Da Dama Sun Ɓace Yayin Da Jirgin Ruwa Ya Kife A Sakkwato
Kungiyoyin ceto da ta suka haɗa da jami’an NIWA, da hukumar NEMA, da hukumar SEMA ta jiha, da kuma Red Cross sun shiga aikin ceto da bincike domin gano waɗanda ake zargin sun ɓace. Bello ya bayyana cewa suna ci gaba da wayar da kan al’ummomin da ke zaune a bakin ruwa kan muhimmancin amfani da rigar kariya/ceto ta ruwa da kuma bin ƙa’idojin zirga-zirga a ruwa.
A ranar 17 ga Agusta, gwamnatin jihar ta tabbatar da mutuwar fasinjoji huɗu tare da mutane 41 da aka ceto da kuma mutane biyar da suka ɓace a wani hatsarin jirgin ruwa a ƙauyen Kojiyo, ƙaramar hukumar Goronyo. Haka kuma, a ranar 22 ga Agusta, wani hatsari ya auku a ƙauyen Faji na ƙaramar hukumar Sabon Birni. Wannan ya sa hatsarin ranar Juma’a ya zama na uku a cikin wata guda.
Shugaban Sashen Ceto da Farfaɗo da NEMA, Malam Tukur Abubakar, ya tabbatar da cewa ana ci gaba da aikin ceto domin gano fasinjan da ake nema. Wani mazaunin yankin, Malam Abubakar Jabbi daga La, ya ce masu linƙaya sun ceto mutane tara, sun kuma hango gawar mutum ɗaya, yayin da ake ci gaba da neman gawar wata mata da ta nutse.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp