Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur ta amince da daukar dan wasan Paris St-Germain Randal Kolo Muani a matsayin aro na tsawon kakar wasa daya, an dade ana danganta dan wasan mai shekaru 26 da kungiyoyin Firimiya, inda ake tsammanin yaje daya daga cikin kungiyoyin Tottenham, Manchester United, Chelsea ko kuma West Ham.
Kolo na shirin komawa Tottenham a ranar karshe ta kasuwar saye da sayarwar yan kwallo bayan kulla yarjejeniyar a sirrance da kungiyar da Thomas Frank ke jagoranta, Kolo Muani ya shafe rabin kakar wasan da ta gabata a matsayin aro a Juventus, inda ya zura kwallaye takwas a wasanni 16 na Seria A.
Tsohon dan wasan gaban Nantes da Eintracht Frankfurt ya koma PSG ne a watan Satumban 2023 kuma ya lashe gasar Ligue 1 har sau biyu, Kolo ya kuma buga wa Faransa manyan wasanni 31, inda ya zura kwallo a gasar cin kofin duniya da ta doke Morocco a wasan dab da na kusa da karshe na shekarar 2022, ya kuma buga wasan karshe da Argentina ta doke su.
Yana shirin zama babban dan wasa na hudu da Tottenham ta dauko a bazara, bayan Mohammed Kudus, Joao Palhinha da Xavi Simons, dan wasan gaban Kolo Muani zai taimakawa Tottenham wajen zura kwallaye yayinda take fatan komawa kan ganiyarta da kuma samun gurbin buga gasar Zakarun Turai a badi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp