Binciken PREMIUM TIMES ya tabbatar cewa jihar Kano ba ta zama jiha ta farko ba wajen samun sakamakon jarrabawar kammala Sakandare SSCE da Hukumar NECO ta fitar a 2025 ba, saɓanin iƙirarin da gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi.
Gwamnan ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa Kano ta zama jiha mafi samun sakamakon mai kyau a, yana danganta hakan da manufofin gwamnatinsa a fannin ilimi. Ya ƙara da cewa Lagos da Oyo sun zo na biyu da na uku. Sai dai bayanai daga NECO sun nuna akasin haka, inda fiye da rabin daliban Kano suka kasa samun sakamako mai kyau.
Bisa ga alƙalumman NECO, cikin ɗalibai 136,762 da suka yi jarrabawar daga Kano, kashi 49.84% kacal ne suka samu mafi ƙarancin CREDIT biyar da suka haɗa da Turanci da Lissafi, yayinda kashi 50.16% suka gaza. Wannan ya sa Kano ta zo matsayi na 29 daga jihohi 37, inda kawai ta fi jihohin Arewa guda takwas kamar Yobe, da Adamawa, da Filato, da Borno, da Jigawa, da Katsina, da Zamfara da kuma Sokoto.
- Makarantun Da Ba Ƙwararrun Malamai Za Su Rasa Zama Cibiyar Rubuta Jarrabawar NECO
- Gwamnatin Kano Ta Mika Ƙorafe-Ƙorafe Kan Sheikh Lawan Triumph Zuwa Majalisar Shura
A haƙiƙanin gaskiya, Abia ce ta fi kowa nasar a jadawalin jahohin, inda kashi 83.31% daga cikin dalibai 11,260 suka samu mafi ƙarancin CREDIT biyar da suka haɗa da Turanci da Lissafi. Jihohin Imo (83.09%), da Ebonyi (80.60%), da Anambra (76.80%) suna bin sahu. Kano ba ta cikin jerin jihohi goma na farko, sai dai tana cikin goman ƙasa.
Alƙalumman sun nuna cewa abin da Kano ta fi kowa da shi, shi ne yawan ɗalibai da suka rubuta jarrabawar, ba nasara ba. Duk da yake Kano ta samu ɗalibai 68,159 da suka yi nasara, an samu ɗalibai 68,603 da suka faɗi – hakan na nuna cewa Kano ta fi da yawan waɗanda suka gaza samun CREDIT 5 fiye da waɗanda suka yi nasara .
Wannan ya tabbatar da cewa iƙirarin gwamnan na Kano ya dogara ne kan adadin masu rubuta jarrabawar, ba ainihin waɗanda suka samu nasara ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp