Gwamnatin tarayya ta yi hadaka da Hukumar Kula da Abinci da Ayyukan Noma ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO), ta hanyar kaddamar da shirin da za a kashe kimanin Naira miliyan 200, domin kara habaka kiwon kifi a fadin wannan kasa.
Manufar kaddamar da shirin ita ce, domin samar da wadataccen kifi a fadin Nijeriya baki-daya.
- Ana Fatan Majalisar Wakilan Amurka Za Ta Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Raya Hadin Gwiwar Sin Da Amurka
- Nazari Kan Littafin Baba Zube Na 5 (Gwamnati)
Darakta a sashen kula da kiwon kifi a Ma’aikatar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasa na Teku, Wellington Omoragbon, a jawabinsa a wajen kaddamar da shirin a yankin Eriwe da ke Jihar Ogun ya sanar da cewa, an kaddamar da shirin a karkashin aikin kiwon kifi na ‘FISH4ACP’.
Omoragbon, wanda Darakta na biyu a ma’aikatar ya wakilce shi a wajen taron ya bayyana cewa, manufar shirin ita ce, domin a kara samar da kudade a fannin da kumakokarin ci gaba da gudanar da kiwon na kifi a wannan kasa.
Kazalika, ya yaba wa Hukumar ta FAO da kuma sauran abokan hadaka, bisa tallafa wa kasar nan, musamman ta fuskar kara habaka harkokin kiwon kifin.
Ya kara da cewa, duba da irin dimbin Kogunan da ake da su a wannan kasa, idan aka yi amfani da su yadda ya kamata, za a iya bunkasa fannin na kamun kifi a Nijeriya.
Omoragbon ya ci gaba da cewa, kalubalen da ake ci gaba da fuskanta a halin yanzu shi ne, na karancin kudade da kuma ci gaba da samun hauhawar farashin abincin da ake ciyar da kifin, wanda wannnan babban kalubale ne da masu sana’ar ke ci gaba da fuskanta a kasar.
“Muna sane da cewa, babban kalubalen da masu sana’ar a kasar nan ke ci gaba da fuskanta shi ne, karancin kudade tare da kuma ci gaba da samun hauhawar farashin abincin kifin, amma za mu iya kokarinmu, domin ganin mun samar wa da masu kiwon dauki, musamman domin a cike gibin da ake da shi a fannin,” a cewar Omoragbon.
hi kuwa a nasa jawabin, wakilin hukumar ta FAO a kasar nan da kuma yankin Afirka ta yamma, Koffy Kokako, kira ya yi da a dauki matakan da suka dace, domin kawo karshen shigo da kifi kimanin tan miliyan biyu da ake yi daga kasashen waje zuwa cikin wannan kasa.
Ya bayyana cewa, tarayyar turai da sauran abokan hadaka; sun zuba kudaden ne, domin masu kiwon kifi a kasar, su samu damar samun kudaden da za su yi kiwon kifin tare kuma da kara bunkasa kiwon kifin a kasar.
Haka nan, ya kara da cewa, a kashi na farko na aikin masu kiwon kifi guda 40 ne aka bai wa daga Naira miliyan 2.5 zuwa Naira miliyan biyar, wanda jimillar kudin suka kai kimanin Naira miliyan 200.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp