Kasar Sin ta yi watsi da rahoton da MDD ta fitar, game da batun kare hakkokin bil adama a jihar Xinjiang ta kasar Sin, tana mai bayyana rahoton da tarin karairayi, wadanda aka kitsa domin amfani da su a matsayin makamin siyasar Amurka da kasashen yamma.
Da yake tsokaci game da hakan a yau Alhamis, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce fitar da rahoton mai cike da rashin gaskiya, da ofishin babban kwamishinan MDD mai lura da kare hakkokin bil adama ya yi, ya tozarta darajar ofishin. (Saminu)