Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wasu matasa biyu da suka nutse yayin wanka a rafin da ke Hayin Yawa Gada, ƙaramar hukumar Tudun Wada ta jihar.
Mai magana da yawun hukumar, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2 na rana a ranar Alhamis, 9 ga Oktoba, 2025. Ya ce ofishin hukumar da ke Tudun Wada ya samu kiran gaggawa daga jami’in Hisbah wanda ya sanar da cewa matasan da suka nutse sun kasance Habu Sani da Haruna Isah, dukkansu masu shekaru kusan 15.
“Da jami’anmu suka isa wurin, sun gano cewa matasan sun shiga ruwa domin wanka amma suka kasa fita. An ciro su cikin halin suma, daga baya kuma aka tabbatar da mutuwarsu,” in ji Abdullahi.
Jami’an hukumar sun miƙa gawarwakin ga ƴansanda na sashin Tudun Wada domin gudanar da bincike. Haka kuma, hukumar ta gano gawar wani mutum da ba a san ko wanene ba a wata rijiya da ke Jaba Masaƙa Shago Tara a cikin birnin Kano, bayan samun rahoton kiran gaggawa daga ofishin ƴansanda na Kwalli.
Shugaban hukumar, Sani Anas, ya yi kira ga iyaye da shugabannin al’umma da su riƙa kula da ƴaƴansu tare da hana su zuwa wuraren ruwa, musamman a lokacin damina domin kare rayukansu daga irin wannan masifa.