Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu bayan janye jerin sunayen mutanen da za a yi wa afuwa biyo bayan ce-ce-ku-cen jama’a.
Gwamnatin ta sanar da cire sunayen masu laifuka irin su masu garkuwa da mutane, masu safarar miyagun ƙwayoyi, da sauran masu manyan laifuka daga jerin bayan jama’a sun yi ƙorafi.
- Sakamakon Nazarin CGTN Ya Yabawa Gudunmuwar Sin Ga Dunkulewar Yankin Asiya Da Pasifik
- An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest
Da yake mayar da martani ta hannun mai taimaka masa kan hulɗa da jama’a, Phrank Shaibu, Atiku ya ce gwamnatin Tinubu tana yanke shawara ne bayan jama’a sun bayyana ɓacin ransu.
“Shugaba Tinubu ya janye gafarar da ya yi wa masu safarar miyagun ƙwayoyi da masu garkuwa da mutane, amma bayan ‘yan Nijeriya sun yi ƙorafi har suka tashe shi daga barcin da yake yi. Wannan sauyi ba hikima ba ce, abin kunya ne,” in ji Atiku.
Ya tambayi waye ya amince da jerin farko, da kuma dalilin da ya sa gwamnati ta yi tunanin sakin masu manyan laifuka.
“Ba wasa ba ne yi wa mutane afuwa. Ya kamata ta zama alamar adalci da muradun ƙasa, ba dama ga masu aikata laifi ba,” in ji shi.
Atiku ya ce wannan lamari ya nuna cewa gwamnatin ba ta da tsari, sannan ya buƙaci a wallafa cikakken jerin sunayen mutanen da aka fara yi wa afuwa domin ‘yan Nijeriya su san gaskiya.














