Tun fil azal, manoman kasar nan na yin noma da damina da kuma rani, inda suke noman ranin domin kara samun kudi.
Manoman suna noma amfanin gona iri-iri, inda hakan ya kara sa ake kara bunkasa tattalin arzikin kasar da kuma samar da ayyukan yi, musamman a tsakanin matasa da mata.
- Wani Abun Fashewa Ya Tarwatse A Wani Masallaci Ya Kashe Akalla Mutane 18 A Afganistan
- Wani Abun Fashewa Ya Tarwatse A Wani Masallaci Ya Kashe Akalla Mutane 18 A Afganistan
A bisa wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa, akwai hanyoyi da dama da za a yi amfani da su domin habaka noman shinkafar a kasar nan.
Wasu manoma da ke jihar Kano sun ce yawancin mutane sun fi siyan shinkafar waje, saboda ta fi haske duk da cewa, shinkafar da ake nomawa a kasar nan, ba ta da wata illa da za ta shafi kiwon lafiyar ‘yan Adam da ke yin amfani da ita.
“Mutane sun fi siyan shinkafar waje saboda ta fi haske duk da cewa, shinkafar da ake nomawa a kasar nan, ba ta da wata illa za ga kiwon lafiyar ‘yan’adam”.
A cewarsu, sai dai manoman na fuskantar matsalar samun isasshen takin zamani saboda, takin da gwamnati ke rabawa ba ya kaiwa ga manoma.
“Manoman na fukantar matsalar samun isasshen takin zamani saboda, takin da gwamnati ke rabawa ba ya kai wa ga manoma. Sun kara da cewa, akasari manyan moma ne ke sayen takin, inda hakan ke kara sanya wa takin ke kara yin nisa ga kananan manoma da ke yin noma a jihar”.
An bayyana cewa mahukunta a jihar Kano da ke kula da yadda ake tafiyar da noma a jihar sun ce gwamnatin jihar na yin iya kokarinta wajen tallafa wa manoman da ke jihar ta hanyoyi daban-daban.
A cewar mahukuntan, gwamnatin jihar a karkasin Abdullahi Umar Ganduje, ta samar wa matasa manoma a jihar takin zamani a kan farashi mai sauki.
Sun kara da cewa, gwamnatin ta kuma samar wa da manoman jihar hanyoyin yin noma a zamanance, musasam don a kara bunkasa noman shinkafar da ake nomawa a kasar nan.
“Gwamnatin ta kuma samar wa da manoman jihar hanyoyin yin noma a zamanance, musamman don a kara bunkasa noman shinkafar da ake nomawa a kasar nan”.
Har ila yau, manoman shinkafar a jihar bisa wani bincike da aka yi, ya nuna cewa, manoman a jihar, na fuskantar kalubalen samun injinan zamani da manoman za su yi amfani da su wajen nomann nata da kuma rashin ta.