Kasa da ‘yan makwanni kalilan da samun nasarar tikitin takara na jam’iyyar sa, dan takarar gwamnan Jihar Ogun a karkashin lemar Peoples Redemption Party (PRP), Farfesa David Olufemi Bamgbose, ya mutu.
Dattijon mai shekara 54 a duniya ya kasance mai taimakon al’umma kuma Farfesa ne a sashin ilimi (education) ya mutu ne a ranar Juma’a a asibitin Sacred Heart da ke Lantoro, Abeokuta, inda aka kwantar da shi domin jinyar gajeruwar rashin lafiya da ta sameshi.
- Zulum Ya Shigar Da Marayu 7000 Makaranta A Monguno
- Yadda Rugujewar Gadar Katarko Ta Katse Yobe Da Jihohin Borno Da Gombe
LEADERSHIP ta labarto cewa a ranar Alhamis ne marigayi Bamgbose ya yi korafin rashin lafiya inda makusantansa suka garzaya da shi wani asibiti mai zaman kansa da ke rukunin gidajen ‘yan gaju (FHE) da ke Olomoore a yankin Abeokuta yayin da kuma aka canza masa asibiti zuwa babban asibitin Gwamnatin tarayya (FMC) da me Abeokuta.
Hadimin mamacin, Oduntan Olayemi, shine ya tabbatar da mutuwar mai gidan nasa a lokacin da ke zantawa da ‘yan jarida a Abeokuta, ya yi bayanin cewa an sanya marigayin a na’urar da ke taimakawa numfashi a asibitin Sacred Heart har zuwa ranar Juma’ar lokacin da rai ya yi halinsa.
Ya ce kafin ya mutu ya yi ta harba numfashi sosai inda aka yi kokarin kula da shi amma kwana ya kare.
Bamgbose dai ya fice daga jam’iyyar PDP inda ya shiga cikin PRP a kwanakin baya.
Kafin nan a zaben 2015 ne ya kasance dan takarar gwamna na jihar Ogun a karkashin jam’iyyar APGA.
Ya kasance wanda ya lashe zaben fitar da gwani na jam’iyyar PRP na zaben 2023 da ke tafe wanda aka gudanar a ofishin NUJ da ke Iwe Irohin, Abeokuta, babban birnin jihar.
Marigayin Farfesa ne a jami’ar European America University, kafin mutuwarsa babban Minista ne a cocin Peace and Love Church of God, da ke yankin Ogbe a cikin Abeokuta, ya mutu ya bar matarsa Misis Mary Bamgbose da yara shida.