Gwamnatin Jihar Zamfara ta ɗauki sababbin malamai 500 gwamnati, a wani yunƙuri na ci gaba da farfaɗo da sashin ilimi a faɗin jihar. Shugaban hukumar kula da aiyukan ma’aikata ta Jihar Zamfara kuma shugaban kwamitin ɗaukar ma’aikata, Aliyu Mohammed Tukur, ne ya bayyana haka, yana mai cewa tsarin ɗaukar aikin ya kasance mai tsauri da cancanta.
A cewarsa, mutane 11,708 ne suka nemi aikin koyarwa ta hanyar manhajar yanar gizo ta gwamnati, inda daga cikinsu 8,184 suka cika sharuɗɗan farko kuma aka tantance su. Daga cikin wannan adadi, mutane 3,105 ne suka shiga jarabawar kwamfuta (CBT), sannan 1,033 daga cikinsu suka samu shiga tantancewar baki da baki ta ƙarshe. Bayan nazari da kimantawa, mutane 500 aka zaɓa domin ɗauka a matsayin malamai a makarantun jihar.
Tukur ya ce sababbin malamai sun kware a fannoni masu muhimmanci kamar Turanci, Lissafi, Kimiyya, da kuma Koyon Sana’o’i (Vocational Studies). Ya kuma yabawa Ma’aikatar Ilimi, da Kimiyya da Fasaha bisa jajircewarta wajen tabbatar da nasarar tsarin ɗaukar aikin. “Wannan ɗaukar aiki babbar nasara ce wajen magance ƙarancin malamai da kuma inganta ingancin ilimi a makarantun gwamnati,” in ji Tukur.
Ya ƙara da cewa gwamnati za ta tura sababbin malamai zuwa makarantun da ke ko’ina cikin jihar, tare da bai wa yankunan karkara da waɗanda ba su da isassun malamai fifiko. Wannan mataki, a cewarsa, yana cikin shirin gwamnatin jihar na tabbatar da cewa kowane yaro a Zamfara yana samun ingantaccen ilimi, ba tare da bambanci ba.














