Al’ummar Tudun Yola a ƙaramar hukumar Gwale ta jihar Kano, sun shiga alhini bayan wasu da ba a gano su waye ba suka kashe wasu mata biyu sannan suka banka wa gidansu wuta. Matan da suka rasu su an bayyana sunayensu da Hauwa’u Yakubu da Zahra’u Aliyu, mata ga Alhaji Ashiru Shu’aibu Usaini.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun fara kai wa matar farko hari da wuƙa kafin daga bisani su kunna wutar da ta ƙone gidan gaba ɗaya. Anas Shu’aibu, ɗan uwa ga mamatan, ya shaida wa manema labarai cewa lamarin ya faru ne ranar Laraba da misalin ƙarfe 12 na rana, lokacin da mijin da ƴaƴansa ke wuraren aikinsu.
- Shugaban APC Na Kano Ya Nemi Afuwa Daga Al’ummar Fagge Kan Kalamansa
- NSCDC Ta Cafke Mutum Biyu Bisa Zargin Satar NAPEP Da Safarar Miyagun Kwayoyi A Kano
A cewarsa, sun fara zaton gobara ce ta haddasa mutuwar matan, sai da bincike ya tabbatar cewa farmakarsu akai, sannan aka yi ƙoƙarin ɓoye alamar laifi ta hanyar ƙona gidan. Ya ce sun tarar da gawar ɗaya daga cikin matan a ƙone, yayin da suka tarar da ta biyun a cikin banɗaki bayan sun karya ƙofar da ƙyar.
Alhaji Ashiru ya bayyana baƙin cikinsa tare da roƙon hukumomin tsaro su gano waɗanda suka aikata wannan ta’asa. Ya ce bai san dalilin da yasa aka kai musu hari ba, yana mai kira da yi masa tabbatar da adalci.
Kakakin rundunar ƴansanda ta Kano, CSP Abdullahi Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa ana ci gaba da bincike domin gano waɗanda ke da hannu a wannan mummunan aiki.














