Gwamnatin Tarayya ta yaba wa Al’ummar Duniya kan Fasahar Ilimi (ICEDT) saboda ba da gudunmawarsu wajen ci gaban tsarin ilimi a Nijeriya.
Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, wanda ya jaddada muhimmancin fasaha wajen tsara makomar kasa a fannin ilimi, ya bayyana haka ne yayin da ma’aikatar ta kaddamar da matakin gwaji na shirin horar da ‘Malaman kan Fasahar Wucin Gadi (AI)’.
- Ƙungiyar IPOB Ta Yi Watsi Da Hukuncin Ɗaurin Rai-Da-Rai Ga Nnamdi Kanu
- Sace ‘Yan Makarantar Mata Ta Kebbi: Abubuwan Da Ba A Fada Ba
A jawabin da ya yi ranar Talata a Abuja a wajen bikin kaddamar da shirin gwamnati da kuma babban mataki a kokarin da ake yi na daidaita koyarwa da koyo da bukatun tattalin arzikin dijital na karni na 21, Alausa ya ce gudunmawar da ake bayarwa, wacce take nufin horar da malamai da basira da kwarewa wajen hada mafita ta AI cikin tsarin ilimi na Nijeriya, duk yabon da za a yi musu ba zai wadatar ba.
An wakilce shi ta Sakatare, Mista Abel Enitan, Alausa ya bayyana cewa malaman Kwalejojin Tarayya na Hadin Kai, wadanda su ne farko da za su amfana, suna da matsayi na musamman da na dabaru a fannin ilimi na kasa, saboda haka suna wakiltar ka’idojin inganci, daidaito da kirkire-kirkire.
Ya ce: “Ina karfafar duk mahalarta da su shiga cikin horon cikin himma saboda ana sa ran matakin gwaji zai samar da rahotanni da za su jagoranci fadada shirin zuwa dukkan yankunan siyasa guda shida.
“Wannan shiri wata kofa ce ta ci gaban fasaha a fannin ilimi a duk fadin kasa, kuma ina kira ga malamai su yi amfani da wannan dama sosai domin su zama zakakuran da za su yada ilimin AI a fannin ilimi ga sauran abokan aikinsu.”
A jawabinta, Daraktar Sashen Tallafin Ilimi, Mrs. Larai Nana Ahmed, wacce Mataimakiyar Darakta na Sashen Tallafin Makarantu, Mrs. Ogbuke Njideka Dorothy ta wakilta, ta maimaita jajircewar ma’aikatar wajen hade fasahar dijital cikin bangaren ilimi.
Ta bayyana cewa shirin ya dace da Dabarun Fasahar Ilimi na Kasa (National EdTech Strategy) da kuma hangen nesa na Gwamnatin Tarayya na shiryawa dalibai don fuskantar gaskiyar tattalin arzikin dijital.
A cewarta, malamai su ne zuciyar wannan sauyi, shi ya sa aka yanke shawarar fara horon da Kwalejojin Tarayya na Hadin Kai, wadanda ke zama fitilar ilimi na sakandare a Nijeriya.
A yayin isar da sakon fatan alheri, Shugaban Huldar Dabaru da Masanin Koyo a ICEDT, Dr. Abdurrahman Orasanye, ya bayyana wannan shiri a matsayin muhimmin mataki a tafiyar hadin gwiwa na sauya ilimi ta hanyar kirkire-kirkire.
Ya sake tabbatar da jajircewar ICEDT wajen tallafa wa Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya da sauran masu ruwa da tsaki wajen horar da malamai Nijeriya da kwarewar da ake bukata domin samun nasara a duniya mai amfani da fasahar dijital.














