Wani masanin tsaro da leken asiri, Yahuza Getso, ya bayyana cewa kashi 99 cikin 100 na dukkan ’yan bindiga da ke aiki a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya ’yan Nijeriya ne.
Getso ya kuma jaddada cewa hukumomin tsaro sun san wadannan ’yan bindiga, sun san su da kuma inda suke.
Masanin tsaron ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Morning Brief na Channels Television.
A cewarsa, “kashi 99.9 cikin 100 na ’yan bindigar da ke aiki a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya ’yan Nijeriya ne. Mun san su, mun san su waye, mun san inda suke. Ba a wani boye suke ba ko a wani wuri mai wahalar isa.”
Ya yi wadannan bayani ne bayan sace dalibai 25 daga Sakandiren Gwamnati ta Maga, a Jihar Kebbi, da kuma kashe Birgediya Janar Musa Uba a Jihar Borno.
Jaridar LEADERSHIP ta tunatar da cewa harin makarantar ta Kebbi ya faru ne misalin karfe 4 na safiyar Litinin, lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kutsa cikin makarantar, inda suka kashe mataimakin shugaban makarantar kuma suka sace dalibai mata 25.
Rahotanni sun nuna cewa mazauna yankin sun kasance cikin shirin ko-ta-kwana bayan samun bayanai na yiwuwar hare-hare a wasu kauyuka makwabtansu a ranar da ta gabata, amma hakan bai hana maharan kutsa yankin ba, lamarin da ya jefa al’umma cikin tsoro da alhini.
Haka kuma, Birgediya Janar Uba, wanda a farko Rundunar Sojin Nijeriya ta bayyana cewa yana cikin koshin lafiya bayan an yi masa kwanton-bauna da kungiyar ISWAP a kan hanyar Damboa–Biu a Jihar Borno, daga bisani an tabbatar da mutuwarsa.
Kungiyar ISWAP a ranar Talata ta saki hotuna da ke nuna ikirarin cewa ita ce ta kama kuma ta kashe babban jami’in.














