Dan Majalisar Wakilai na Amurka Riley Moore ya yi Allah wadai da sace yara sama da 300 da malamai 12 daga Makarantar Katolika ta St. Mary da ke Jihar Neja, yana mai kira ga gwamnatin Nijeriya da ta “kawo karshen ‘yan bindiga Fulani masu tsattsauran ra’ayi da ke addabar Yankin Arewa ta Tsakiya.”
“A matsayina na uba, ganin wadannan hare-haren na sace-sacen kananan yara, ya jefa ni cikin damuwa,” Moore ya wallafa a wani rubutu a shafinsa na X a ranar Asabar.
- Yadda Za Ki Kara Wa Kanki Tsawon Gashi
- Yadda Wasu Mahukunta Ke Amfani Da Muƙamansu Wajen Musguna Wa Al’umma
Kalaman Moore na zuwa ne a matsayin martani ga sace mutane da aka yi a Makarantar Firamare da Sakandare ta Katolika ta St. Mary da ke Papiri, karamar Hukumar Agwara, Jihar Neja.
A cewar Kungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN), an sace dalibai 303 da malamai 12 a safiyar Juma’a, bayan wani bincike da aka gudanar.
Wannan lamari ya biyo bayan hare-hare makamancin haka a yankin, yayin da ‘yan kwanaki da suka gabata, aka sace ‘yan mata ‘yan makaranta 25 a Jihar Kebbi, kuma wasu hare-haren ‘yan bindiga sun karu a fadin Nijeriya
ADVERTISEMENT














