Gwamnatin Jihar Kaduna ta ƙara jaddada kudirinta na jawo masu zuba jari na ƙasa da ƙasa zuwa jihar.
Yayin da yake gabatar da Jawabi a taron koli na manyan ‘yan kasuwa na duniya wanda ya gudana a kasar Afrika ta Kudu, Gwamna Uba Sani ya gabatar da jihar Kaduna a matsayin jihar da tafi dacewa wajen zubar jari a Nijeriya.
- Yaushe Ne Ƙarshen Rikicin Yajin Aiki Tsakanin ASUU Da Gwamnatin Tarayya A Nijeriya?
- Wasu Kura-kurai Da Matan Aure Ke Yi Ke Sa ‘Yan Aiki Aure Mazajensu
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai, na jihar Kaduna Malam Ahmed Maiyaki, ya fitar, ya ce taron wanda Hukumar Kula da Zuba Jari ta Nijeriya (NIPC) da Ofishin Jakadancin Nijeriya tare da haɗin gwiwar MTN suka shirya, ya samu halartar manyan masu zuba jari na duniya, da jami’an gwamnati na matakai daban-daban.
A cewar sanarwar, Gwamna Sani ya gabatar da Jihar Kaduna a matsayin jihar da ta fi dacewa da zuba jari a Nijeriya, wadda aka gina bisa sauye-sauyen manufofi, kwanciyar hankali, dokoki da yanayin kasuwanci mai sauƙi. Ya bayyana muhimman fannonin zuba jari guda huɗu kamar Noma, Sufuri, Ma’adinai da Makamashin Sabuntawa wanda su na daga cikin ginshiƙan dabarun ci gaban jihar.
Gwamnan ya kuma gana da shugabannin wata masana’antar tace ƙarafa masu daraja da ke Afirka ta Kudu, PMT Inda ta gabatar da tayin haɗin gwiwa ta hannun Kamfanin Samar da Ma’adinai na Kaduna (KMDC) domin saka hannun jari a ɓangaren ma’adinai da fasaha, gina ƙwarewa, da aiwatar da shirin kafa cibiyar tarawa da sarrafa ma’adinai a Kaduna.
Sanarwar ta ƙara da cewa, gwamnan ya tabbatar da cewa, ƙofar Kaduna a bude take ga masu zuba jari waɗanda ke bin ka’idoji masu dorewa tare da mayar da hankali kan samar da darajar dogon lokaci.
Hakazalika, sanarwar ta kuma ruwaito Gwamna Uba Sani yana yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa sauye-sauyen da suka inganta yanayin zuba jari a Najeriya tare da ƙarfafa jihohi wajen neman haɗin gwiwar ƙasashen duniya.














