Tawagar ‘yan wasan Nijeriya ta Super Eagles ba ta samu tikitin zuwa gasar cin kofin duniya ba da za a yi a Amurka da Mexico da kuma Canada a shekara ta 2026 mai kamawa.
Hakan ya biyo bayan da Jamhuriyar Congo ta fitar da ita a wasan karshe a cike gurbi daga yankin Afirka da ci 4-3 a bugun fenariti, bayan da tun farko suka tashi 1-1 bayan minti 120.
- Wasu Kura-kurai Da Matan Aure Ke Yi Ke Sa ‘Yan Aiki Aure Mazajensu
- Yadda Za Ki Kara Wa Kanki Tsawon Gashi
Nijeriya ta kai wasan karshe bayan doke Gabon 4-1 ranar Alhamis, yayin da Jamhuriyar Congo ta fitar da Kamaru a dai ranar., sakamakon da ya ba su damar karawa a tsakaninsu a daren ranar Lahadi a kasar Moroco.
Yanzu haka Jamhuriyar Congo za ta hadu da wasu tawagogi shida daga wasu nahiyoyin a cikin watan Maris a Mexico, domin fitar da biyun da za su cike gurbin shiga wasannin da kasashe 48 za su fafata.
Wasu na cewa Argentina ce za ta sake lashe kofin duniya a badi, bayan da Super Eagles ta kasa kai bantenta. Sai dai hakan ba ya nufin tawagar Nijeriya tana takawa Argentina birki idan sun hadu.
Tawagar ‘yan wasan kasar Argentina mai rike da kofin duniya da ta lashe a Katar a 2022 tana daga fitattun da ke wakiltar wasannin a koda yaushe, wadda jimilla tana da uku a tarihi.
Wannan shi ne karon farko da Nijeriya ta kasa samun tikitin shiga gasar cin kofin duniya karo biyu a jere a tarihi tun bayan da ta fara halartar wasannin a shekarar 1994, wadda karo uku tana kai wa zagaye na biyu a wasannin.
Kenan Super Eagles, wadda ta buga gasar kofin duniya sau shida daga tara baya, ba ta je wasannin da aka yi a 2006 da 2022 da 2022 ba, ga kuma yanzu ba za ta yi karawar 2026 ba.
Argentina ta lashe kofin duniya a 1978 da kuma 1986 a lokacin da Nijeriya ba ta fara zuwa wasannin ba, sannan Argentina ta dauki kofi na uku a 2022 da aka yi a Katar, gasar da Super Eagles ba ta samu tikitin shiga ba.
Daga gasa 18 da Argentina ta halarci gasar cin kofin duniya ta yi ta biyu a 1930 da 1990 da kuma 2014, haka kuma ta yi nasarar cin wasa 47 daga wasa 88 da ta buga a babbar gasar kwallon kafar ta duniya.
Hakan ne ya sa wasu ke cewa Argentina ce za ta sake daukar kofin na duniya a badi, saboda Super Eagles ba ta samu tikitin shiga wasannin ba.














