Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta samu nasarar doke abokiyar karawarta Ikorodu United da ci 2-1 a wasan Mako na 14 da suka buga a filin wasa na Muhammad Dikko dake birnin Katsina.
Wannan ne karo na farko da Pillars din ta samu nasara a wasanni 8 da ta buga na baya bayan nan a gasar ta Firimiyar Nijeriya, Pillars ta hada maki 9 kacal a wasanni 14 da ta buga a bana yayin da take cigaba da zama a kasan teburi.
Kyaftin Rabiu Ali na Kano Pillars ne ya zura kwallon farko a ragar Ikorodu United tun a minti na 2 da fara wasan, kwallon ita ce ta 4 da Ali ya ci wa Pillars a bana, a minti na 30 Suleiman Idris ya sake ci wa Pillars kwallo kafin Joseph Arumala ya farkewa Ikorodu kwallo daya dab da tafiya hutun rabin lokaci.
Wannan nasarar ta Pillars bai hanata cigaba da zama a matsayi na 20 na teburin gasar Firimiyar Nijeriya, amma kuma kocin Pillars Babaganaru na fatan ganin kungiyar ta bar kasan teburin ba da jimawa ba.














