Dakarun rundunar Operation Whirl Stroke sun kama wani da ake zargin mai garkuwa da mutane mai suna Abubakar Bawa, a Jihar Taraba.
An cafke shi ne yana ƙoƙarin tserewa daga ƙaramar hukumar Wukari a Jihar Taraba.
- Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin: Taron COP30 Ya Shaida Niyyar Sassan Kasa Da Kasa A Fannin Tinkarar Matsalar Sauyin Yanayi
- Kano Pillars Ta Samu Nasarar Farko A Wasanni 8 Da Ta Buga
An kama shi ne yayin samamen Operation Zafin Wuta, aikin da ke nufin kawar da ɓarayi da ’yan ta’adda da ke addabar al’ummomi a kudancin Taraba.
Sojojin sun ce Bawa na da alaƙa da wani shugaban masu garkuwa da mutane, Umar Musa, wanda aka kama a ranar 22 ga watan Nuwamba 2025.
Bincike ya nuna cewa su biyun na cikin wata babbar kungiya da ke da hannu a sace-sace da kai hare-hare a yankin.
Kwamandan Runduna ta 6, Birgediya Janar Kingsley Uwa, ya yaba wa sojojin bisa jajircewa da ƙwarewarsu.
Ya ce wannan kame na nuna cewa aikin yana tafiya yadda ya kamata.
Rundunar sojin ta buƙaci jama’a su kasance masu lura su kuma riƙa bayar da sahihan bayanai.
A halin yanzu ana tsare da wanda ake zargin, yayin da ake ci gaba da bincike a kansa.














