Majalisar Wakilai ta sha alwashin bankado yadda aka fasa gidan yarin kuje a ranar 5 ga watan Yuli, wanda aka danganta harin da kungiyar ‘yan ta’adda ta ISWAP.
Shugaban Kwamitin Tsaro da Bayanan Sirri na Majalisar Wakilai, Sha’aban Sharada, ne ya bayyana hakan yayin zaman bincike tare da jin ba’asi game da harin da ‘yan ta’adda suka kai a gidan yarin na Kuje da ke Abuja.
- Miyetti Allah Ta Roki Soludo Ka Da Ya Soke Kiwon Shanu A Jiharsa
- Kotu Ta Bai Wa Kwamishinan Gona Wa’adin Kwana 2 Ya Dawo Da Tirakta 58 Da Ya Sayar A Zamfara
Tun a ranar 22 ga watan Yuli ne dai Majalisar Wakilai ta kafa kwamitin hadin gwiwa kan tsaro da binciken sirri da kwamitoci masu alaka da tsaro don bincikar musabbabin harin da aka kai wa gidan yarin na Kuje.
Sharada, wanda shi ne shugaban kwamitin hadin gwiwar, ya tabbatar wa jama’a cewa mambobin kwamitin ba za su bar lamarin ya wuce haka kawai sakaka ba ba tare da daukar matakan da suka dace ba.
Ya ce majalisar za ta binciki lamarin da ya haddasa faruwar lamarin, inda ya ce za a yi kokari matuka don tabbatar da samar da tsaro a cikin ginin gidan gyaran halin da kewayensa.
Ya ce, za a samar da matakan da za a kiyaye sake afkuwar lamarin a nan gaba da sauran sassan kasar nan.
Ya ce, majalisar za ta kuma tabbatar da bin diddigin matakan da za a bi don kare rayuka da dukiyoyin mazauna babban birnin tarayya, Abuja da na daukacin Nijeriya.
Ya kuma tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa kwamitin hadin guiwar zai yi tsayin daka don aiwatar da aikin da aka dora masa alhaki.
Ya ce an samu bayanai masu ma’ana daga manyan daraktocin ma’aikatar harkokin gwamnati da hukumar leken asiri ta kasa da sauran hukumomi da ke bada bayanai ga hukumomin tsaro a Nijeriya.
Kwamitin, ya ce zai sake gayyatar shugabannin tsaro da sauran shugabannin hukumomin tsaro ciki har da wasu ministocin da suka kasa amsa gayyatar da aka yi musu a baya.