Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutane uku a sakamakon hatsarin mota mai ɗauke da man fetur da kuma gobarar wani gini daban, duka a ranar Juma’a.
A cewar sanarwar ACFO Saminu Yusif Abdullahi, hatsarin farko ya faru ne da misalin ƙarfe 1:30 na rana a kan titin Zariya kusa da Kasuwar Kura. Tankar mai ɗauke da kimanin lita 30,000 ta kife ta kama da wuta, inda direban ya buge wani mai keke amma ya tsira, sai dai mutane ukun da aka tarar a sume daga baya an tabbatar da mutuwarsu.
- Yadda Gobara Ta Lashe Kasuwar Katako Ta Gwambe
- Manyan Ma’aikatan FIRS 4 Sun Rasu Sakamakon Gobarar Da Ta Tashi A Ginin Afriland A Legas
Hukumar ta ce jami’anta tare da haɗin gwuiwar ƴansanda da hukumar kiyaye haɗurra sun yi nasarar kashe gobarar da ceto mutane, sannan suka miƙa gawarwakin ga ASP Ahmad Lawan na Ofishin ƴansanda na Kura. Motoci biyu na kashe gobara daga shalƙwatar ofishin Kura ne suka yi aikin ceton. A halin yanzu ana ci gaba da bincike don gano musabbabin hatsarin.
Kimanin da ƙarfe 2:45 na rana, an sake samun gobara a wani ginin kasuwanci bene biyu a Hamisu Plaza, unguwar Tarauni, a kan titin Maiduguri. Sanarwar ta bayyana cewa shaguna uku ne gobarar ta shafa kai tsaye, yayin da sauran shagunan na ƙasa aka yi nasarar kare su. Motar kashe gobara daga filin bikin baje koli (Trade Fair) ta taimaka wajen kashe wutar, kuma har yanzu babu cikakken bayani kan abin da ya jawo gobarar.
Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta jihar, Alhaji Sani Anas, ya shawarci jama’a su kula da yadda suke amfani da wuta musamman a lokacin hunturu, tare da yin kira ga direbobi da su yi taka-tsantsan a hanya. Ya ce bin ƙa’idojin tuki da guje wa sakaci na iya hana aukuwar manyan haɗurra da ke janyo hasarar rayuka da dukiyoyi.














