… ci gaba daga makaon da ya gabata.
4:- Saka suturar da zai fito da surar ta: Kada ki ji kunyar taka mata birki muddin kika fahimci cewa ‘yar aikinki tana son rika shiga irin wacce za ta rika fito da surarta a gaban mijinki.
Ana iya samun wani wasu halittunta da suka fi naki da maigida zai iya gani wanda hakan zai zama tarkon da za ta kama shi da su.
5:-.Daukar ‘yar aiki da ta fi ki kyau: Duk kuwa da namiji a wani lokacin ba kyawun mace bane a gabansa ba. Amma daukar ‘yar aikin da ta fiki kyau tamkar kin gayyato wa kanki matsala ne da kanki. Gara dai wacce kika fi kyau koda wani abu ya kasance za a zarge shi amma ba ke ba.
6:- Bai wa ‘yar aiki damar kai wa mijinki abinci: Cikin sauki ‘yar aikin da take son aure miki miji za ta iya amfani da wannan damar domin ganin ta ciyar da shi wani shirin da za ta iya juya masa kansa ya ji ita yake so.
7:- Wulakanta baki a gabanta: Idan kina wulakanta bakin mijinki a gaban ‘yar aikinki Ita kuma za ta yi amfani da wannan damar wajen kyautata musu har ta shiga ransu. Hakan kuma zai ba ta damar samun shiga wajen mijinki cikin sauki ta hanyar wadannan da kike wulakanta wa ita kuma tana dadada musu.
8:- Wanke masa kayan ciki: Akwai wani sirri na musamman na wanke kayan ciki. Duk ma’auratan da suke wanke wa kansu kayan ciki soyayya da kauna na musamman na kara shiga tsakaninsu. Don haka idan kika bar ‘yar aikinki ita ke wanke masa kuma ta goge masa sai ta ji a ranta inama ita ce matarsa. Don haka ki kiyaye.
9:- Ba ta damar yin hira da mijinki: Idan kika bai wa ‘yar aiki mai wayo damar yin hira da mijinki cikin sauki za ta iya aure miki miji. Domin za ta iya amfani da kalaman da ta san ba kya masa domin jawo hankalinsa.
10:-Rashin baiwa miji lokaci: Idan kin kasance irin matan nan ne da suka damu da harkokin gabansu amma ba su damu da kula da miji ba to a kwana a tashi za ki tsinci kanki cikin matan da ‘yar aiki ta aure mazajen su.













