A wani sabon martani da ya fito daga ofishinsa, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya yi kira ga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da ya daina siyasantar da batun tsaro, yana mai cewa abin da ake buƙata shi ne aikin gwamnati mai ma’ana don magance matsalolin da suke addabar jihar. Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin jihar ta zargi Sanata Barau da yin magana da ka iya kawo cikas ga ƙoƙarin tsaro, zargi da ya ce ba shi da tushe balle makama.
Sanata Barau, ta bakin mai magana da yawunsa Ismail Mudashir, ya ƙalubalanci gwamnati da ta fito fili ta nuna bidiyon da ake cewa ya yi magana da ke tayar da tarzoma. Ya jaddada cewa a dukkan lokuta yana aiki tare da hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki wajen magance barazanar ƴan fashi da hare-haren da ake fuskanta a wasu sassan jihar Kano da ƙasar baki ɗaya. Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta karkatar da hankalinta daga gudanar da mulki yadda ya kamata zuwa yaɗa kalaman da ba zasuyi amfani ga al’umma.
- Barau Zai Yi Ƙarar Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Gawuna/Garo Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Dala Miliyan 10
- ‘Yansanda Sun Ƙaryata Rahoton Kashe Ɗan Wasan Barau FC A Katsina
Sanata Barau ya ce rashin daidaito a gwamnati ya sanya Kano ta rasa matsayinta na zama sahun gaba wajen ci gaba a Nijeriya, inda ya buƙaci Gwamna Abba ya tashi tsaye wajen mayar da jihar kan tafarkin ci gaba. Ya kuma yi nuni da gudunmawar da ya bayar a fannin tsaro, ciki har da samar da motocin aiki, da babura ga jami’an tsaro, da gina ofisoshin ƴansanda, da kuma taimakawa hukumomin DSS, da NSCDC, da Immigration ta hanyar kawo cibiyoyin horo a Gwarzo, da Kabo da Bichi.
Ya ƙara da cewa fitilun tituna na Sola da ya saka a ƙananan hukumomin Kano Arewa da sauran yankuna ya taimaka wajen inganta aikin ƴan sintiri da rage laifuka. A cewarsa, irin waɗannan aiyuka su ne ya kamata gwamnatin jihar ta na yi, maimakon neman ɓata masa suna. Ya buƙaci gwamnatin Kano da ta yi koyi da irin wannan jajircewa wajen tabbatar da tsaro da ingantaccen mulki ga al’ummar jihar.













