Babban sakataren kwamitin koli na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin (CPC) Xi Jinping, ya jaddada muhimmancin inganta hanyoyin tafiyar da harkokin intanet na dogon zango.
Yayin da yake jagorantar zaman nazari na ofishin siyasa na kwamitin koli na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin a jiya Jumma’a, Xi ya yi kira da a ci gaba da kokari don samar da yanayi mai tsabta, da lafiya da kuma inganci a shafin intanet.
Da yake jaddada muhimmancin rawar da kula da tafiyar da intanet ke takawa a cikin harkokin gudanarwa na kasa, Xi ya jaddada bukatar karfafa cikakken tsarin gudanarwa da kuma karfafa ayyukan da aka tsara a karkashin jagorancin kwamitin koli na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin na bai-daya.
Ya jaddada bukatar karfafa jagoranci ga dandalolin shafin intanet, da masu watsa labarai masu zaman kansu, da kamfanoni masu mabambantan tashoshin sadarwa a intanet, tare da karfafa su su sauke nauyin inganta walwalar jama’a da ke wuyansu, da kuma zama masu watsa abubuwa masu kyau.
Da yake nuni da cewa kula da tafiyar da shafin intanet kalubale ne na bai-daya ga dukkan kasashen duniya, ya jaddada mahimmancin hadin gwiwa tsakanin kasashen don yaki da haramtattu da miyagun laifuka a kan shafin intanet da kuma habaka gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai-daya a fannin harkokin intanet. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














