ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Jihar Zamfara Na Da Rinjaye A Fannin Noma, In Ji Gwamna Lawal A Taron AIF Na Morocco

by Sulaiman
3 weeks ago
Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sake jaddada wa duniya cewa Jihar Zamfara na da babbar damar bunƙasa harkokin noma, yana mai cewa noma ne ginshiƙin ci gaban tattalin arzikin jihar da Arewa maso Yamma gaba ɗaya.

 

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Gwamnan Jihar Zamfara Sulaiman Bala Idris ya fitar a ranar 29 ga watan Nuwamba, inda ya ce, Gwamna Lawal ya yi wannan bayani ne yayin da ya halarci Babban Taron Masu Zuba Jari na Afirka (AIF), Ranakun Kasuwar Zuba Jari na 2025 da aka gudanar daga ranakun 26 zuwa 28 ga watan Nuwamba, 2025, a birnin Rabat da ke ƙasar Morocco.

ADVERTISEMENT
  • Xi Ya Jaddada Muhimmancin Inganta Hanyoyin Kula Da Tafiyar Da Intanet Na Dogon Zango
  • Hong Kong Ta Yi Jimamin Wadanda Gobara Ta Shafa Ta Hanyar Saukar Da Tutoci

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta ce taron ya haɗa manyan masu zuba jari daga sassa daban-daban na Afirka, inda aka tattauna manyan yarjejeniyoyin kasuwanci tare da lalabo hanyoyin aiwatar da ainihin zuba jari a faɗin nahiyar.

 

LABARAI MASU NASABA

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

Sanarwar ta ce, taron, wanda Bankin Raya Afirka tare da haɗin gwiwar wasu manyan cibiyoyi guda shida ke jagoranta, ya mayar da Taron Zuba Jari na Afrika a matsayin dandali na musamman da ke hanzarta tsara manyan ayyukan ci gaba da tara kuɗaɗen da za su tafiyar da su a Afirka.

Zamfara

A yayin taron, Gwamna Lawal ya halarci manyan tattaunawa kan yadda za a bunƙasa zuba jarin kamfanoni masu zaman kansu ta hanyar samar da yanayi mai sauƙi, da kuma zaman muhawara kan faɗaɗa zuba jari ta tsarin haɗin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu, tare da tattaunawa kan yadda za a tara jarin cikin gida domin ingiza ci gaban Afirka.

 

A gefe guda kuma, Gwamnan ya rattaba hannu kan wata muhimmiya Yarjejeniyar Fahimtar Juna tsakanin Gwamnatin Jihar Zamfara da Hukumar ‘Ministry of Finance Incorporated’ (MOFI) domin haɓaka gagarumin shirin sauya fasalin noma a jihar.

 

Yarjejeniyar ta sanya Zamfara a cikin jihohin da za su fi cin gajiyar shirin INTEGRANIUM na ƙasa, wanda ke mai da hankali kan noma na zamani, sarrafa amfanin gona, hanyoyin adana bayan girbi da kuma buɗe hanyoyin fitar da kayayyaki zuwa kasuwannin duniya.

 

A ƙarƙashin yarjejeniyar, Gwamnatin Jihar Zamfara za ta samar da filaye, ababen more rayuwa, tsaro da manufofi masu sauƙi, yayin da MOFI za ta jagoranci samo kuɗaɗen zuba jari, jawo hankalin masu zuba jari, da tallafa wa aiwatar da manyan ayyukan noma.

 

Ana sa ran wannan haɗin gwiwar zai samar da dubban ayyukan yi, ya ƙara wadatar abinci, ya ƙarfafa darajar amfanin gona tare da hanzarta ci gaban tattalin arziki mai shafar talakawa a Zamfara da yankin Arewa maso Yamma gaba ɗaya.

 

Da yake jawabi ga masu zuba jari a wani zagayen tattaunawa, Gwamna Lawal ya bayyana Zamfara a matsayin cibiyar noma ta haƙiƙa, yana mai cewa gwamnatinsa na samun gagarumar nasara a fannoni daban-daban.

Zamfara

A cewarsa, “Ina matuƙar farin ciki da ganin Bankin Raya Afirka tare da sauran manyan masu zuba jari na duniya sun halarci wannan taro. Noma ne gaba ga Afirka, Nijeriya da kuma Zamfara musamman, saboda yalwar damar da ake da ita. A Zamfara, noma shi ne rinjayenmu. Muna noman kusan dukkan nau’o’in amfanin gona; ba mu tsaya kan wake ko waken soya kaɗai ba. Muna da yalwatacciyar ƙasa mai albarka.

 

“Ina gayyatar dukkan masu zuba jari na duniya su zo Zamfara. A halin yanzu muna matakin ƙarshe na kammala filin jirgin saman ƙasa da ƙasa na jigilar kaya, muna gina otel mai matsayi na biyar, tare da manyan ayyukan sabunta birane a faɗin jihar.”

 

Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa na ɗora babban alheri kan noma a matsayin ginshiƙin wanzar da ayyukan yi ga matasa, rage talauci da tabbatar da tsaron abinci mai ɗorewa a Zamfara.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tinubu
Manyan Labarai

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa
Labarai

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli
Labarai

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Next Post
Shugabar Kasar Iceland:Taron Koli Na Mata Na Duniya Na Da Matukar Ma’ana Ga Kasashe Daban Daban

Shugabar Kasar Iceland:Taron Koli Na Mata Na Duniya Na Da Matukar Ma’ana Ga Kasashe Daban Daban

LABARAI MASU NASABA

Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.