’Yan bindiga sun kai hari ƙauyen Kururawa da ke yankin Lakwaya a ƙaramar hukumar Gwarzo, Jihar Kano, a daren ranar Lahadi.
Sun isa garin ne a kan babura biyu daga Jihar Katsina.
- Za A Fara Gasar Wasanni Ta Nakasassu Da Masu Bukata Ta Musamman Ta Sin
- Salah Ba Ya Cikin ‘Yan Wasan Liverpool Da Za Su Kara Da Inter Milan
Sun kutsa cikin gidan wani dattijon manomi, Alhaji Yakubu Na Tsohuwa inda, suka tafi da shi.
Ɗansa babba, Badamasi, ya samu raunin harbin bindiga a ƙafa yayin da yake ƙoƙarin hana su tafiya da mahaifinsa.
Yanzu haka yana asibiti inda likitoci ke kula da shi.
Mutanen yankin sun ce ƙauyen na kusa da iyakar Katsina, don haka yana fuskantar barazanar hare-hare.
Sun roƙi Gwamnatin Kano ta gaggauta kafa sansanin tsaro a yankin.
Rundunar ’Yansandan Kano ba ta fitar da sanarwa kan lamarin ba tukuna, kuma ba a samu damar tattaunawa da kakakin rundunar ba.














