An ruwaito cewa an riƙe sojojin Nijeriya 11 a Burkina Faso bayan jirginsu ya yi saukar gaggawa.
Sojojin suna kan hanyarsu ta zuwa ƙasar Portugal.
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga, Sun Ceto ’Yan Kasuwa A Sakkwato
- Za A Fara Gasar Wasanni Ta Nakasassu Da Masu Bukata Ta Musamman Ta Sin
Burkina Faso, tare da Mali da Nijar, sun fice ƙungiyar ECOWAS, inda suka kafa sabuwar ƙungiya mai suna Alliance of Sahel States (AES) bayan dakatar da su saboda juyin mulki da sojoji suka yi a ƙasashensu.
AES ta ce jirgin sojin Nijeriya ya shiga sararin samaniyar Burkina Faso ba tare da izini ba, kuma jirgin ya tsaya a birnin Bobo-Dioulasso ranar 8 ga watan Disamba, 2025.
Jirgin na da ma’aikata biyu da fasinjoji tara, waɗanda duk sojoji ne.
Hukumomin Burkina Faso sun tabbatar cewa jirgin bai samu izinin shiga ƙasarsu ba.
AES ta bayyana wannan hakan a matsayin “keta ikon ƙasa” kuma ta ce ta sanya tsaro a sararin saman ƙasarta don daƙile kowane jirgi daga shiga ƙasar.
Ba a fayyace ko sojojin Nijeriya na cikin rundunar ECOWAS da aka tura Benin bayan yunƙurin juyin mulki ba.
Masana harkokin diflomasiyya sun ce wannan lamari na iya ƙara tashin hankali tsakanin ECOWAS da AES, waɗanda yanzu suka raba gari kan siyasa da tsaro.














