Shugaban Amurka Donald Trump ya kausasa caccakar da yake yi wa kasashen Turai, yana mai bayyana nahiyar a matsayin mai rauni da ta fara lalacewa, saboda manufofinta masu cike da dimbin kura-kurai a kan shige da ficen baki ko kuma ‘yan ci rani.
Tsamin dangantakar da ake samu tsakanin shugaba Trump da Turai ta kara bayyana ne a yayin wata hira da ya yi da jaridar Politico da ke Amurka, wadda aka wallafa a ranar Litinin, inda ya bayyana manufofin kasashen Turai kan tunkarar matsalar kwarara bakin haure a matsayin marasa fa’ida.
- Trump Ya Yi Alƙawarin Dakatar da Shigowar Masu Hijira Daga Matalautan Ƙasashe
- Fadar Shugaban Ƙasa Ta Zargi Turaki Da Cin Amanar Nijeriya Saboda Kiran Trump Ya Kawo Wa PDP Ɗauki
Trump ya bayyana Birtaniya da Faransa da Jamus da Poland da kuma Sweden a matsayin kasashen da ya ce yanzu haka kwararar ‘yan gudun hijirar na yin mummunan tasiri kan tattalin arziki da kuma zamantakewarsu.
Shugaban na Amurka ya kuma soki rawar da kasashen na Turai ke takawa a kokarin kawo karshen yakin Rasha da Ukraine, inda ya zarge su da fada babu cikawa a daidai lokacin da yakin ke kara rincabewa.
A lokacin da aka tambaye shi ko Amurka za ta yi watsi da kawance da kasashen na Turai idan suka gaza rungumar manufofin gwamnatinsa kan bakin haure? sai Trump ya kada baki ya ce lokaci ne kawai zai fayyace makomar alakar ta su.














