ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Kashe Mutum 4 A Rikicin ‘Yan Kungiyar Asiri A Anambra

by Rabi'u Ali Indabawa
9 months ago
Anambra

Mutum hudu ne suka rasa rayukansu a harin tashin hankali da ya faru a kusa da Afor Market Junction a kauyen Nawfia, cikin Karamar Hukumar Njikoka, Jihar Anambra.

Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Anambra, SP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin.

  • EFCC Ta Kama Tsohon Gwamnan Anambra Chris Ngige A Abuja
  • Ƴansanda Sun Zafafa Farautar Mambobin Ƙungiyar Asiri Ta ‘Sai Malam’ A Sakkwato

Ikenga ya ce harin ya samo asali ne daga rikicin kungiyoyin asiri masu hamayya da juna, yana mai karawa da cewa wasu daga cikin mambobin kungiyar daya, wadanda ke amfani da motar Black Ledus Jeep mai lambar da “ba a sani ba”, sun mamaye kasuwar Afor Nawfia suka harbe mutum ba tare da tantancewa ba.

ADVERTISEMENT

Ya ce ‘yan ta’addan sun tsere kafin isowar ‘yansanda, amma bayanan farko da aka tattara a wurin sun bayar da muhimman bayanai, kuma Rundunar tana aiki a kai don tabbatar da an gano masu laifin kuma an kama su.

Sanarwar ta ce a wani bangare, “Rundunar ‘Yansanda ta Jihar Anambra na son bayar da cikakken bayani kan harin da ya shafi kungiyoyin asiri da ya faru a yammacin ranar 7 ga Disamba, 2025, a kasuwar Afor Nawfia, a kan tsohon titin Onitsha zuwa Awka.

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

“Idan za a iya tunawa cewa, kwanaki hudu kafin wannan lamari, jami’an rundunar da ke cikin Special Anti-Cult Skuad, Enugwu-Ukwu, bisa sahihan bayanai kan shirin rikicin kungiyoyin asiri masu hamayya, sun kama mutum biyu masu hadari kuma sun karbi bindiga daga gare su.

“Mutumn da aka kama suna ba ‘yansanda muhimmiyar bayanai domin hana wasu tashin hankali na kungiyoyin asiri a cikin Awka da kewaye. Duk da wadannan matakai na rigakafi da jami’an rundunar suka dauka, wani mamba daga wannan kungiyar guda daya, a yammacin ranar 7 ga Disamba, 2025, yana amfani da mota Black Ledus Jeep mai lamba da ba a sani ba, sun mamaye kasuwar Afor Nawfia suka harbi mutum.”

“Wannan harin tashin hankali ya yi sanadin mutuwar mutum hudu, bayan haka ‘yan ta’addan sun tsere daga wurin. Ko da yake sun tsere kafin isowar ‘yansanda, bayanan farko da aka tattara a wurin sun bayar da muhimmiyar jagora, kuma Rundunar tana aiki a kai don tabbatar da cewa an gano masu laifin kuma an kama su.”

Ya bayyana cewa Rundunar tana da kudurin kawar da kungiyoyin asiri, laifuka masu tashin hankali da duk wani nau’in laifi a jihar.

“Za a sanar da karin bayani yayin da bincike ke ci gaba,” in ji shi.

Majiyoyi daga yankin sun ce lamarin ya jawo rudani yayin da mutane suka yi ta tserewa domin neman tsira, tare da karawa da cewa wasu mutanen sun mutu har lahira sakamakon harbin bindiga.

Wata majiya ta ce, “‘Yan ta’addan da ke rike da makamai sun mamaye Afor Market Junction sannan nan da nan suka fara harbi, suka kashe mutane da yawa. Babu wanda ya san dalilin harin, amma lamarin ya girgiza al’ummarmu.”

Wasu mazauna da suka bayyana ra’ayinsu kan lamarin sun ce har yanzu suna cikin tashin hankali, inda da dama ke kiran a kara tsaro a yankin.

Wani shaida a kusa da wurin ya ce, “Halin da aka shiga gaskiya ya rikita mutane. Masu kai harin sun fito daga wurin da babu wanda ya sani a wannan yammacin suka fara harbin kaio mai uwa da wabi

“‘Yansanda sun kaddamar da bincike kan harin kuma suna aiki don kama masu laifin.”

Hotunan bidiyo na lamarin da ake yadawa a Intanet sun nuna mazauna suna gudu domin tsira, yayin da wasu gawawwaki ke kwance a cikin jini a kasa.

Anambra
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja
Labarai

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Next Post
Wakilin Musamman Na Shugaban Kasar Sin Ya Halarci Taron Kasa Da Kasa Na Shekarar Zaman Lafiya Da Aminci A Turkmenistan

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.