Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da kafa Runduna ta Musamman ta tsaro domin kare tashoshin mota da sauran muhimman wuraren taruwar jama’a a faɗin jihar, a wani mataki na daƙile barazanar tsaro da ke ƙaruwa.
Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Lahadi, inda ya ce matakin ya nuna ƙudirin gwamnati na hana shigowar miyagu musamman ta manyan hanyoyin shiga da fita cikin birnin Kano.
- Kotu Ta Umarci EFCC Ta Biya Wani Ƴan Kasuwar Kano Miliyan 5, Ta Nemi Afuwar Su
- ’Yan Bindiga Sun Sace Manomi, Sun Jikkata Ɗansa A Ƙauyen Kano
Sanarwar ta bayyana cewa rundunar za ta gudanar da tsauraran sintiri, da tattara bayanan sirri, da hada-hadar aiki tsakanin hukumomin tsaro a tashoshin mota da sauran wuraren da ake ganin suna da haɗari, ciki har da gidajen mai da wuraren taruwar matafiya.
Gwamna Yusuf ya ce wannan mataki na rigakafi ne domin daƙile barazanar tsaro tun kafin ta ta’azzara, yana mai jaddada manufar gwamnatinsa ta nuna rashin sassauci ga aikata laifuka da kuma ƙarfafa haɗin gwuiwa tsakanin hukumomin tsaro domin dawo da ƙwarin gwuiwar jama’a.














