Attajirin nan na Nijeriya kuma Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya ƙaryata rahotannin da ke cewa Amurka na adawa da aikin Matatar Man Fetur ta Dangote, yana mai cewa Shugaban Amurka Donald Trump “ya fi kowa farin ciki” da wannan matata.
Dangote ya bayyana cewa Amurka ba abokiyar hamayya ba ce ga matatar, illa ma tana daga cikin manyan ƙasashen da ke cin gajiyar aikinta, domin ta samar da kaso mai yawa na ɗanyen man fetur da matatar ke amfani da shi. Ya ce kasuwancin man fetur tsakanin ƙasashen biyu na da anfani ga ɓangarorin biyu.
- Trump Ya Caccaki Kasashen Turai Bayan Ayyana Nahiyar A Matsayin Mai Rauni
- Shugaba Xi Ya Fayyace Muhimmiyar Matsayar Sin Dangane Da Batun Taiwan Yayin Zantawarsa Da Shugaba Trump
Da yake magana a Lekki, Legas, Dangote ya ce ƙarancin samar da ɗanyen mai a Nijeriya ne ya sa matatar ke sayo mai daga ƙasashen waje ciki har da Ghana da Amurka. A cewarsa, Nijeriya ba ta iya biyan buƙatunta na cikin gida da kanta a halin yanzu.
Ya ƙara da cewa Nijeriya na sayen sama da ganga miliyan 100 na ɗanyen mai daga Amurka duk shekara, kuma adadin na iya ƙaruwa zuwa ganga miliyan 200 idan an samu ƙarin wadata. Dangote ya jaddada cewa wannan mu’amala ta kasuwanci ce ke sa Trump ya kasance mai goyon bayan matatar, ba kamar yadda ake yaɗawa a kafafen sada zumunta ba.














