Jami’an tsaro na hadin-gwiwa karkashin ‘Operation MESA’ sun ceto mutum uku daga cikin mutane biyar da aka sace a lokacin wani harin ‘yan bindiga da daddare a karamar hukumar Gwarzo ta jihar Kano.
Rundunar ta hadin-gwiwa ta hada da sojojin rundunar soji ta 3, rundunar sojin sama ta Nijeriya (NAF) da rundunar ‘yansandan Nijeriya (NPF).
- Shugaba Xi Ya Jaddada Muhimmancin Bunkasa Aikin Tarbiyantar Da Yara
- El-Rufai Ya Ƙaryata Rahoton Goyon Bayan Yanki Ko Wani Mutum A Zaɓen 2027
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, an sace mutanen ne a daren Lahadi lokacin da wasu mutane dauke da makamai da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka kai hari a kauyen Lakwaya da ke karamar hukumar Gwarzo.
Da yake martani kan lamarin, Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a na rundunar soji ta 3, Kyaftin Babatunde Zubairu, ya tabbatar da ceto mutane uku, daga cikin wadanda aka sace yayin da ake ci gaba da kokarin ceto sauran biyun.
Kyaftin Zubairu ya tabbatar wa jama’a cewa, rundunar ta hadin gwiwa sun kuduri aniyar ceto dukkan mutanen da aka sace cikin koshin lafiya.
ADVERTISEMENT














