Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya dakatar da cire tallafin man fetur a watannin ƙarshe na gwamnatinsa bayan tattauna dalilan tsaro kan shirin wanda zai yi dagula zaman lafiyar da ake da shi a kasar.
Hakan na kunshe ne a cikin wani sabon littafi mai suna ‘Daga Soja zuwa Ɗan Siyasa: kyawawan abubuwan da Muhammadu Buhari ya gadar’, wanda Dr. Charles Omole, Darakta Janar na Cibiyar Bincike Kan Manufofin ‘Yansanda da Tsaro (IPSPR) ya rubuta.
- Da Ɗumi ɗumi: Mafarkin Nijeriya Na Zuwa Gasar Kofin Duniya Na Dab Da Cika
- Me Ya Sa Aka Kayyade Yin Amfani Da Sinadaran Narkar Da Kankara A Beijing
An gabatar da littafin ne a Abuja ranar Litinin a wani taron da Shugaba Bola Tinubu da sauran jami’an gwamnatinsa da na baya suka halarta.
A cewar littafin, an gudanar da tattaunawar tsaro a gab da karshen gwamnatin Buhari kan yiwuwar cire tallafin man fetur kafin miƙa mulki ga gwamnati mai zuwa.
Littafin ya ambaci shugaban hukumar Ma’aikatar tsaron cikin gida (DSS), Yusuf Bichi, yana gargaɗin cewa, cire tallafin a wannan lokacin na iya haifar da tarzoma a duk faɗin ƙasar. Bichi ya kuma yi gargaɗin cewa, lamarin na iya haifar da yanayi da ka iya ƙarfafa yin juyin mulki.














