Yau Alhamis 18 ga watan Disamba ne, aka fara aiwatar da matakan kwastam na musamman a dukkanin fadin yankin cinikayya cikin ’yanci na Hainan, wanda hakan ya zamo sabon muhimmin mataki a manufar kasar Sin ta fadada bude kofarta ga duniya a sabon zamanin da muke ciki.
Ganin yadda ake kara aiwatar da manufofin gata na kwastam, da saukaka matakan kasuwanci gami da zirga-zirgar ababen hawa, da kuma kyautata ayyukan sa ido yadda ya kamata, aiwatar da matakan kwastam na musamman a dukkanin fadin yankin cinikayya cikin ’yanci na Hainan, zai iya haifar da dimbin alfanu ga kamfanoni, da daidaikun mutane, har ma da habakar tattalin arzikin duniya baki daya, al’amarin da ya janyo mabiya da masoya da dama a duniya.
Tun tuni kamfanoni masu jarin waje, sun fara gudanar da ayyukansu a lardin Hainan, ganin yadda za su samu sabbin damarmaki, saboda fara aiwatar da matakan kwastam na musamman a dukkanin fadin yankin cinikayya cikin ’yanci na Hainan. Alkaluma sun nuna cewa, daga watan Janairu zuwa Satumban bana, adadin jarin waje da aka yi amfani da shi a lardin Hainan, ya karu da kaso 42.2 bisa dari, kan na makamancin lokaci na bara.
Kazalika, ayyana ranar 18 ga watan Disambar bana don fara aiwatar da matakan na da babbar ma’ana. Saboda a makamanciyar ranar a shekarar 1978, cikakken zama na uku na kwamitin kolin JKS na 11, ya kafa tarihin kaddamar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofar kasar Sin ga duniya.
A halin yanzu, wato bayan shekaru 47, ra’ayin nuna bangaranci, da na ba da kariyar cinikayya na kara kamari, har ma dunkulewar tattalin arzikin duniya baki daya na fuskantar koma-baya. A irin wannan halin da ake ciki, fara aiwatar da matakan kwastam na musamman a dukkanin fadin yankin cinikayya cikin ’yanci na Hainan ya kafa tarihi, wanda ya zama wani muhimmin mataki da kasar Sin ta dauka, wajen inganta bude kofa ga duniya, da kafa budadden salon raya tattalin arzikin duniya. (Murtala Zhang)














