Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya kaddamar da wani sabon farmaki a kan hukumar NMDPRA, yana mai dagewa kan cewa; shugabancin hukumar na yin zagon kasa ga kokarin da ake yi na bunkasa matatun mai a cikin gida.
A wani taron manema labarai da ya kira a ranar Lahadi a matatar mai ta Dangote, ya ce; ana amfani da shigo da mai daga kasashen waje ne, domin rage karfin tasirin na cikin gidan tare da samar da ayyukan yi a kasashen wajen, yayin da ‘yan Nijeriya ke fafutukar bunkasa nasu masana’antun.
- Gwamnan Zamfara Ya Naɗa Farfesa Ibrahim Tsafe A Matsayin Sabon Shugaban Jami’ar ZAMSUT
- Bunkasar Masana’antun Kasar Sin Ya Kai Kaso 6.0% a Watanni 11 Na Farkon Shekarar Bana
“Ba kuna amfani da shigo da mai don gazawar na cikin gida ba ne”, in ji shi. Daga nan, sai Dangoten ya kuma zargi shugabancin hukumar NMDPRA da kawo cikas ko nakasu ga matatun mai na cikin gida ta hanyar ci gaba da ba da bayar da lasisin shigo da man fetur, “duk kuwa da karuwar da samu na karfin tace man a cikin gida”.
A cewar Dangote, matakin da hukumar ta dauka ya dore kan dogaron Nijeriya na shigo da mai da kuma hana saka hannun jari a cikin gida.
Dangote ya ninka sukar da ya yi wa hukumar, inda ya yi kira da a binciki babban jami’in hukumar ta NMDPRA, Injiniya Farouk Ahmed.
Har ila yau, ya yi ikirarin cewa; an bayar da lasisin shigo da mai da ya kai kimanin kusan lita biliyan 7.5, a rubu’in farko na shekarar 2026, duk da fafutukar da matatun cikin gida ke yi na samun riba.
Dangote ya kuma yi zargin cewa; Injiniya Ahmed, na rayuwa fiye da yadda ya kamata ya yi, yana mai cewa; ‘ya’yansa hudu na zuwa makarantun sakandare a kasar Switzerland tare da kashe miliyoyun daloli a can.
Ya kara da cewa, zarge-zargen na haifar da matukar damuwa game da rikice-rikice masu jan hankali da kuma bukatar sa ido kan ka’idoji a bangaren mai.
“Ba ina kira da a tsige shi ba, kawai don a gudanar da tsattsauran bincike ne,” in ji Dangote, ya kuma kara da cewa, “Ya kamata a bukaci ya yi la’akari da abin da ya aikata, da kuma tabbatar da ganin cewa; bai cutar da ‘yan Nijeriya ba.
Dangoten ya kuma bukaci hukumar da’ar ma’aikata da sauran hukumomin da abin ya shafa, da su binciki lamarin, inda ya kara da cewa; a shirye yake wajen bayar da hujjojin da za su tabbatar da ikirarin nasa, idan an kalubalance shi.
Ya kuma yi gargadin cewa, ci gaba da shigo da man da ake tacewa, yana cutar da man da ake tacewa a cikin gida tare da dora matatun mai a kan hanyar durkushewa. Ya kuma soki abin da ya bayyana a matsayin kafuwar muradun da ke cin gajiyar shigo da mai da ake amfani da shi wajen ci gaban kasa.
Dangane da farashi kuma, Dangote ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa; farashin mai zai kara faduwa, inda ya bayyana cewa; za a sayar da man a kan farashin da bai wuce Naira 740 ba daga ranar Talata, wanda zai fara daga Legas, bayan rage farashin zuwa Naira 699 ga kowace lita. Ya ce, gidajen mai na MRS ne za su fara aiwatar da wannan sabon farashin.
Ya ci gaba da cewa, matatar man ta rage mafi karancin bukatar saye, domin samun dama ga ‘yan kasuwa su shiga a dama da su, sannan kuma ta shirya tura motocinta na CNG a duk fadin kasar, domin tabbatar da samun kudaden shiga.
Dangote ya kara da cewa, a karshe ‘yan Nijeriya za su ci gajiyar tataccen mai na cikin gida, duk da cewa; masu shigo da mai suna yin asara. Ya sake nanata shirin jera sunayen matatar man Dangote a kasuwar canji ta Nijeriya, domin bai wa ‘yan kasa damar mallakar hannun jari a cibiyar. Ya kara da cewa, “Ba zan taba karaya ba, domin kuwa wannan matatar mai ta farko, ta ‘yan Nijeriya ce.”
Har kawo yanzu dai, babu wani bayani a hukumance daga hukumar ta NMDPRA kan wannan zargi, har zuwa lokacin da aka aka hada wannan rahoto. Lokacin da aka tuntubi mai magana da yawun hukumar ta NMDPRA, George Ene-Ita, cewa ya yi babu wani sharhi da zai yi.
Tun lokacin da matatar Dangote ta fara aiki a watan Janairun 2024, mai masana’antar ya yi ta fama da hukumar NMDPRA.
Rikicin ya fara ne a watan Yulin 2024, lokacin da Babban Jami’in Hukumar NMDPRA, Injiniya Farouk Ahmed, ya bayyana cewa; man da ake samu daga matatun mai na cikin gida, ciki har da na Dangote, ba su da inganci idan aka kwatanta da wadanda ake shigowa da shi daga waje.
Ya kuma yi nuni da cewa, matatar man har yanzu tana mataki na farko, sannan kuma ba ta da lasisin gudanar da cikakken aiki. Kana kuma, ya zargi Dangote da neman yin babakere, wajen hada-hadar kasuwancin man.
Bayan haka, Dangote ya karyata ikirarin nasa game da ingancin samfur man, sannan kuma majalisar wakilai ta kaddamar da bincike tare da kira da a dakatar da Ahmed game da kalaman nasa.
Haka zalika, a cikin watan Agusta, hukumar NMDPRA ta ci gaba da nanata cewa; ba a bai wa matatar lasisin kama aiki ba, amma ta ci gaba da aiwatar da ayyukanta.
A cikin Oktoban 2025, tawagar Ahmed ta ci gaba da cewa; hukumar NMDPRA ta kyale masu tace man na cikin gida su samar da man dizal mai samfurin sulfur, har zuwa watan Janairun 2025, kamar yadda ECOWAS ta bayar da dama.
Sai dai, gwaje-gwajen da Dangote ke sa ido ya nuna cewa; man dizal din nasu na da karancin sinadarin sulfur, wanda ya saba wa ikirarin da hukuma ta yi a baya.
A lokacin, majalisar wakilai ta ce; dole ne shugaban NMDPRA ya ci gaba da dakatar da shi, sakamakon furucin da ya yi na yawan sinadarin sulfur da ke cikin man dizal din da yake samarwa a matatar Dangoten, har sai an kammala bincike kan zargin da majalisar ta yi.
An yi wannan kira ne, bayan amincewa da kudirin da dan majalisar wakilai, Esosa Iyawe ya gabatar na muhimmancin jama’a.
Da yake gabatar da kudirin, ya tunatar da cewa; Shugaban Hukumar NMDPRA, ya bayyana cewa, man dizal da matatar Dangote ke samarwa, bai kai wanda ake shigo da shi kasar nan ba, sannan kuma man da yake da shi na da sinadarin sulfur mai yawa.
Ya ce, “A tasu matsayar, Dangote ya yi kira da a yi gwajin nasu man, wanda ‘yan majalisar wakilai suka sa ido a kai, inda aka bayyana cewa; dizal din Dangoten na da sinadarin sulfur da ya kai 87.6, yayin da sauran samfuran dizal guda biyu da aka shigo da su suka nuna cewa, sinadarin sulfur ya wuce karfe 1800 na zuwa 2000, wanda hakan ya sa aka yi watsi da zargin shugaban na NMDPRA.
“An yi zargin cewa, hukumar ta NMDPRA na bayar da lasisi ga wasu ‘yan kasuwa da ke shigo da dizal mai yawan gaske zuwa Nijeriya a-kai-a-kai, sannan kuma; amfani da ire-iren wadannan mai da dizal na iya haifar da babbar illa ga lafiya da kuma hasarar dukiya mai tarin yawa ga ‘yan Nijeriya.”
A gefe guda kuma, bangaren man fetur na Najeriya ya shiga cikin abin ka iya cewa; gaba kura, baya sayaki, masana’antun sun shiga rubibi kan matsalar farashin man; biyo bayan matakin da matatar man Dangote ta yanke na rage farashin man fetur din.
Matakin ya jawo dimbin asara ga masu shigo da mai da kuma masu gidajen man da kuma ‘yan kasuwa, kamar yadda matatar da kanta ta yarda cewa, tana takka asarar makudan kudade.
Binciken da jaridar LEADERSHIP ta yi ya nuna cewa, masu shigo da man fetur daga waje na gab da tafka asarar har ta kimanin Naira biliyan 102.48 a duk wata, bayan rage farashin man fetur daga N828 kan kowace lita zuwa N699, wadda matatar Dangote ta yi.
Haka kuma, an yi hasashen cewa; matatar man za ta yi asarar kusan Naira biliyan 91 a cikin wata guda, sakamakon rage farashin da aka yi kai tsaye, wanda hakan ke nuna tsananin gasar da a halin yanzu ke sake fasalin kasuwacin mai a Nijeriya.
Haka zalika, yayin da ‘yan Nijeriya da dama ke maraba da rage farashin a matsayin wani babban taimako, musamman a lokacin bukukuwan kirisimeti da sabuwar shekara, ‘yan kasuwar man da ke gudanar da ayyukan hakar mai a fadin kasar sun ce; suna kirga asara mai matukar yawa, domin kuwa za a tilasta musu sayar da hannayen jarin da aka saya a kan farashi mai tsada.
Ci gaban ya fallasa manyan laifuffuka masu girma a cikin kasuwar man fetur da aka lalata, tare da masu cin nasara da masu asara kusan a lokaci guda.
Haka zalika, LEADERSHIP ta ruwaito cewa; matatar man Dangote ta sanar da rage farashin man fetur din da Naira 129 a kan kowace lita a ranar Juma’a, inda ta rage a kan tsohon farashin daga Naira 828 zuwa Naira 699 kan kowace lita.
Hakan ya zo ne, kwanaki kadan bayan da matatar man ta bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin samun isasshen man, domin kauce wa layukan da ake samu a gidajen man, musamman a lokutan bukukuwan kirisimeti da na sabuwar shekara. Har ila yau, kamfanin ya ba da sanarwar bayar da lamuni na kwanaki 10 ga masu ‘yan kasuwa, inda ya bayyana cewa; sabon tsarin farashin ya fara aiki tun daga ranar 12 ga Disamba.














