ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shekara Biyar Da Rasuwar Sam Nda-Isaiah

by Sani Anwar
2 days ago
Sam

Kwance-tashi, kamar jiya ne wanda ya kafa LEADERSHIP, Sam Nda-Isaiah, ya mutu, amma kamar yana nan a raye a halin yanzu, wanda bai iya gane hakan ba, shi ne wanda bai san inda na sa gaba ba. Bari in dan sanya muku wasiwasi.

Idan, alal misali, har yanzu kuna da tunanin zai kira ku da misalin karfe 2:30 na dare, domin ya tashe ku ya tambaye ku dalilin da ya sa kuke barci a daidai wannan lokacin, kamar yadda ya saba yi a baya, lokacin ya riga ya wuce, ku dauke shi kawai a matsayin tarihi.

  • Tinubu Zai Gabatar Da Daftarin Kasafin Kuɗin 2026 Ga Majalisun Tarayya
  • PDP Ta Amince Da Jagorancin Turaki, Ta Ce Ta Shiga ‘Sabon Babin Haɗin Kai’

Har ila yau, dariyarsa mai ban sha’awa ko jin muryarsa mai kwarjini yayin da yake tattaro hujjoji cikin zazzafar mukabala, yanzu shiru tun daga ranar 11 ga watan Disamba da daddare, shekaru biyar da suka gabata, na iya zama tamkar wani yanki mai nisa da ya riga ya shude.

ADVERTISEMENT

Duk da haka, wadannan abubuwan tunawa ne, kamar abubuwan da suka faru a Magdalene, kabarin Talpiot a Urushalima bayan wasu karnuka da suka wuce, sun yi kuskure domin suna tunanin Sam a wannan daular, inda ya ke da tasiri mafi girma.

Ba yana tsaka da karatunsa na cikin gida ba ne ko kan hanyarsa ta dawowa daga Hawaii, Beijing, Singapore, ko kuma daya daga cikin wuraren da ya fi son ziyarta ba. Haka kuma, ba yana zaune a kusurwar kujerar da ya fi so mai launin ruwan kasa da ke cikin ofishinsa, yana tafka muhawara da abokansa a kan matsalar Nijeriya ba ne.

LABARAI MASU NASABA

Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma: Martani

Yaduwar Juyin Mulki A Afirka

 

Wani Dandalin

Sam yana rayuwa cikin wata daula ta daban, inda yake da tasiri mafi girma. Sannan kuma, a cikin wannan daula ko dandali, babu wani abin da ya wuce tattaunawa ta yau da kullum, mai cike da jin dadi da walwala ga wadanda suka yi abin da ya dace, za su iya samun wannan kyakkyawar makoma. Dandalin Sam, shi ne shafinsa na mako-mako, (The Last Word).

Kusan na karanta yawancin su kwanan nan, kuma dole ne a yi maka uzuri, don tunanin an rubuta su jiya. Ba ina magana ne game da tarin makalolin da ya tattara ya rubuta, ya kuma buga mai suna ‘Nigeria: Full Disclosure’, a matsayin marubucin jaridar Daily TRUST, kafin kafa LEADERSHIP a 2004 ba. Wannan wani abu ne daban.

Amma duk da haka, a tsakanin fitowar ‘Full Disclosure’ da shekara 10, lokacin da Sam ya dakatar da shafin nasa, domin tsayawa takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ba, ya rubuta wasu abubuwa masu kayatarwa game da abubuwa da dama, tun daga siyasa zuwa mulki, daga cin hanci da rashawa zuwa bangaren shari’a da kuma harkokin kasa da kasa.

 

Karshen maganarsa

Yawancin makalolin sabbbi ne, kuma suna da dadin ji. Dauki mai taken, “Yakin Basasa na PDP,” alal misali. Sam, kasancewarsa Sam, ya yi imanin cewa, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, shi ne babbar matsalar Nijeriya. A jajibirin zaben fid da gwani na jam’iyyar a shekarar 2010, Sam ya yi nazari a kan abubuwa daban-daban, inda ya gano rashin tsarin dimokuradiyya na cikin gida a cikin jam’iyyar ta PDP tun daga tushenta na soja da kuma sace jam’iyyar da Obasanjo ya yi.

Zaben fid da gwani na jam’iyyar PDP na waccan shekarar, ba kamar kowacce ba. Ta kunshi manyan jiga-jigan jam’iyyar, tun daga kan shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida zuwa Janar Aliyu Gusau da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar. Tattaunawar dai, ita ce babbar alamar da ke nuna cewa; siyasar Arewa ta raba gari da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, kuma za ta kai ga “cin amanar” yarjejeniyar da aka yi da wani babban mutum na yin wa’adi daya kacal, bayan kammala wa’adin marigayi Shugaba Umaru ‘Yar’adua.

 

A ba-ta-kashi mai zuwa

Bisa dalilai na kashin kai da na siyasa, Sam, wanda guda ne cikin wadanda suka kafa jam’iyyar Muhammadu Buhari ta CPC, ba ya son PDP ko kadan. Domin kuwa ya ce, kungiya ce ta masu aikata laifuka, wadda mutanen kirkinta kadan ne. Labarin nasa, wanda aka buga kafin zaben fid da gwani na jam’iyyar na 2010, ya kasance mai ban sha’awa.

“Ina ganin yakin da ke zuwa PDP,” in ji shi, “ba za a yi shi da adduna ba, illa kawai za a yi yaki da makaman kare dangi ne (WMD). Sannan kuma, a karshe, yana da matukar amfani ga al’ummar kasa, idan jam’iyyar ta rushe. A halin da ake ciki, ogre ne wanda ba ya amfani da kowa.”

Saboda haka, idan Sam ya yi karin gishiri game da hasashen mutuwar PDP, watakila kuskuren shi ne ta yadda ta rika aiwatar abubuwanta ba tare gudun abin da zai faru ba. Da yawa daga cikin ‘ya’yanta sun canza sheka, amma jam’iyyar, har yanzu tana nan tana neman kashe kanta.

 

Gaskiyar ta’addanci

Sai kuma wani rubutu da ya rubuta a watan Disambar 2010, mai take “Gaskiyar Ta’addanci a Nijeriya.” A lokacin ne kungiyar Boko Haram, duk da cewa; tana kan ganiyarta, ta nuna cewa, zuwa wani dan lokaci kadan ayyukanta na ta’addanci zai ta ci gaba da bazuwa ta hanyar kisa da sauran makamancinsu.

A daidai wannan lokaci ne a shekarar 2009, Umar Farouk Abdulmutallab, dan Nijeriya mai shekara 23, ya yi kokarin tarwatsa wani jirgin sama da ke kan hanyarsa ta zuwa birnin Detroit na Amurka. Shekara guda bayan haka, bama-bamai sun tashi a Jos, Jihar Filato da kuma wasu wurare a Nijeriya, inda suka kashe mutane da dama – wani abu daga cikin kalaman Sam, ya tayar da hankulan wasu kasashe kamar Iraki, Afghanistan da kuma Pakistan.

“Bayan duk kashe-kashen da aka yi a shekarun baya a Jos,” in ji shi, “Kisan 1 ga watan Oktoba a Abuja da kuma kisan gillar da Boko Haram suka yi a Maiduguri, babu wani mai laifi da aka yanke wa hukuncin kisa da kisa. Don haka, dole haka abubuwa za su ci gaba faruwa, har sai mun fara hukunta wadanda suke aikata laifuka.”

Abin bakin ciki, shekara 14 da suka wuce, da dubban mutane suka mutu, miliyoyin mutane suka ji rauni ko kuma suka rasa muhallansu, wasu da yawa kuma suna rayuwa cikin tsoro da fargaba, wasu har yanzu na da tunanin cewa; biyan kudin fansa ga kungiyoyin ‘yan ta’adda shi ne mafi a’ala.

 

Ta cancanci mutuwa?

Sam ya tsani rashin adalci, yanayin da sau da yawa ya kan tsananta a kan batun rashin yin hukunci da kuma cin hanci da rashawa. Bayan shafe watanni yana rubuce-rubuce, don ganin gwamnatin Shugaba Yar’adua ta yi wani abu a kai, Sam ya rubuta wata makala a shekara ta 2008, yana mai kira ga gwamnati ta ayyana “Makon ‘yan damfara na kasa.”

Batun labarin mai taken “Shin Nijeriya Ta Cancanta Mutuwa?” Shi ne abin da Sam ya dauka a matsayin babban rashin adalci da aka yi wa Nuhu Ribadu, wanda ba wai kawai an cire shi a matsayin Shugaban Hukumar EFCC a lokacin ba, har ma an rage masa mukamin dansanda.

Ribadu ya tattake manya-manyan mutane da dama, wajen yaki da cin hanci da rashawa, wanda ba wai kawai yaki da cin hancin ba ne; babban fada ne, karkashin jagorancin dakarun da suka yi garkuwa da Yar’adua.

Tun da laifin da Ribadu ya aikata ya shafi sha’anin alfarma ne, wanda aka kore shi daga aiki maimakon a kara masa girma, Sam ya ba da shawarar cewa; gwamnati ta sanya mako guda da ‘yan damfara za su karbi furanninsu, har ma a shigar da su cikin zauren shahara. “Manyan masu laifi sun amfana da yawa (daga tsarin), fiye da masu gaskiya,” kamar yadda ya rubuta.

Don haka, ga shi al’amarin Ribadu a yau ya canza, kuma ina da yakinin cewa; ba zai taba amincewa rayuwar ‘yan Nijeriya ta shiga cikin wani mummunan yanayi ko hadari ba. Duk da haka, zai yi wuya labarin Ribadun ya nuna irin ainahin irin wahalar da miliyoyin ’yan kasa ke shatare da firgici da tsoro da talauci ba, duk da cewa; yin aiki tukuru kusan shi ne komai.

 

An gama ko a’a?

Idan muka waiwayi baya, za mu ga abin da Sam ya rubuta, mai taken “Koma-bayan Siyasar Arewa,” ko “Atiku Ya Gama,” a wannan lokaci mai daraja da ake ciki. Tabbas akwai manyan ’yan Arewa da suka firgita da rashin shugabanci, wanda hakan ya durkusar da yankin. Amma duk da haka, ’yan Arewan da suka taimaka wajen rage abin da Sam ya rubuta a yanzu suna da ’ya’ya da jikoki da suka shiga sana’ar, ba wai kashe Arewa kadai ba, har ma da hanzari.

Shi kuwa Atiku yana gamawa, fasikancinsa ya zama abin ban mamaki, tare da watsuwa cikin sauran manyan jam’iyyun siyasa, sai dai wadanda har yanzu ba a kafa su ba. Sai dai, watakila har yanzu akwai abin da Atiku ya rage a cikin tankin?

Na kan ji Sam ya ce, “Dan’bura…!” yayin da yake rawa da dariya. Sai kuma ya dan yi jim: “Kai wawa ne, Azu!” yayin da yake sake fashewa da dariya, wanda ko Atiku ma da yana wurin ba zai iya rike tasa dariyar ba!

Ishiekwene, Babban Editan LEADERSHIP, kuma marubucin sabon littafin nan mai suna ‘A Midlifer’s Guide to Content Creation and Profit’.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma: Martani
Bakon Marubuci

Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma: Martani

November 14, 2025
Yaduwar Juyin Mulki A Afirka
Bakon Marubuci

Yaduwar Juyin Mulki A Afirka

November 7, 2025
Raya Al’ada: Bikin Kalankuwa Na 2025 A Kano
Bakon Marubuci

Raya Al’ada: Bikin Kalankuwa Na 2025 A Kano

October 3, 2025
Next Post
’Yan Majalisa Sun Roƙi Tinubu Ya Sake Duba Lamarin Janye Musu ’Yansanda

’Yan Majalisa Sun Roƙi Tinubu Ya Sake Duba Lamarin Janye Musu ’Yansanda

LABARAI MASU NASABA

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025
Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025
Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

December 20, 2025
An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow

An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow

December 20, 2025
Auren Da Ya Fi Auren Gidan Daula Dadi Ga Mace

Auren Da Ya Fi Auren Gidan Daula Dadi Ga Mace

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.