Tsohuwar Uwargidan Shugaban Kasa, Aisha Buhari, ta bayyana cewa jita-jita da suka yadu a cikin Fadar Shugaban Kasa (Billa) a wani lokaci sun sa marigayi mijinta, Muhammadu Buhari, ya fara zargin cewa tana shirin cutar da shi.
Ta ce wannan lamari ya dagula tsarin cin abincinsa tare da ba da gudummawa ga matsalar rashin lafiyar da ta sa ya kaurace wa gudanar da aiki na tsawon watanni a shekarar 2017.
- Wang Yi Ya Zanta Da Ministocin Wajen Cambodia Da Thailand
- Tinubu Zai Gabatar Da Daftarin Kasafin Kuɗin 2026 Ga Majalisun Tarayya
Bayaninta na kunshe ne a cikin sabon littafin tarihin rayuwa mai taken ‘From Soldier to Statesman: The Legacy of Muhammadu Buhari.’ Charles Omole ne ya rubuta littafin, kuma an kaddamar da shi a Fadar Gwamnati (State House) ranar Litinin.
A cewar littafin, Misis Buhari ta ce jita-jitar ta tayar da fargaba a cikin Aso Rock ta haifar da dan rashin amincewa a tsakaninta da Shugaban Kasar na dan wani lokaci.
Ta ce lamarin ya sa ya sauya wasu dabi’unsa na kashin kai, ciki har da kulle dakinsa da kuma rasa wasu lokutan cin abinci. Tsohuwar uwargidan shugaban kasa ta ce tangardar da aka samu a tsarin abinci da aka tsara da kulawa sosai ita ce farkon rashin lafiyarsa.
Mrs Buhari ta bayyana cewa tsawon shekaru ita da kanta take sa ido kan abincin Buhari da karin magunguna (supplements) da yake sha, tsarin da ta ce ya zama dole domin kula da lafiyarsa.
“Wannan ya kasance ne duba da dogon tarihinsa na matsalolin abinci. Rashin lafiyar Buhari ba ta kasance abin asiri ba kuma ba sakamakon guba ba ce,” in ji ta.
Littafin ya bayyana cewa bayan sun kaura daga Kaduna zuwa Fadar Shugaban Kasa, alhakin kula da tsarin abincin Buhari ya koma hannun jami’an gwamnati, lamarin da ya haifar da jinkiri, tsallake lokutan cin abinci, da kuma dakatar da karin magungunan da aka rubuta masa.
A cewar Aisha a cikin littafin, tsawon kusan shekara guda Shugaban Kasar ya daina cin abincin rana akai-akai, inda ta kara da cewa rugujewar tsarin kula da abinci ya raunana shi matuka. Ta ce wannan tabarbarewar ce daga bisani ta haifar da dogwayen tafiye-tafiyen jinya na Buhari zuwa Kasar Birtaniya a shekarar 2017, wadanda suka kai jimillar kwanaki 154, a lokacin da ya mika ikon shugabanci ga Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo.














