Sama da shekaru biyu da suka gabata, masu yin dokoki da jagorori da manoma da kungiyoyi masu zaman kansu da kuma sauran masu ruwa da tsaki a fannin noma, ke ci gaba da yin tsokaci kan tsarin bunkasa fannain noma na Jihar Jigawa.
A makon da ya gabata ne, Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima, ya yi karin haske kan wannan tsari na noma, wanda kuma ya danganta shi a matsayin wani mataki na kara wanzar da zaman lafiya a jihar ta Jigawa da kuma daukacin fadin kasar baki-daya.
- Wang Yi Ya Zanta Da Ministocin Wajen Cambodia Da Thailand
- Yadda Mutanen Gari Suka Lakaɗa Wa Ɗan Majalisa Duka A Zamfara
Kashim ya je Jigawa ne, domin taya mai martaba Sarkin Gumel, Dakta Ahmad Muhammad Sani, muranr cika shekara 45, kan karagar mulkin masarautarsa.
Kazalika, ya danganta saukin da ake ci gaba da samu a fannin tsaro na jihar, kan ci gaba da samar da sauye-sauyen da gwamnatin jihar ke ci gaba da yi a fannin noma na jihar.
Hatta shi ma, Babban Ministan Ma’aiktar Aikin Noma da Samar da Wadataccen Abinci, Abubakar Kyari, na yawan kai ziyarar aiki jihar ta Jigawa, inda yake nuna sha’awarsa kan tsarin na aikin noma, wanda Jigawa ta kirkiro a karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Malam Umar Namadi.
Wannan tsarin, ya wuce batun a takarda kadai, domin ana gudanar da shi ne, a aikace da kuma jingine batun siyasa a gefe guda, wanda hakan ya sanya Ministan ya ayyana Jigawa a matsayin jihar da za a iya samar da wadatacen abinci a kasar nan.
Gwamnan Jigawa Malam Umar Namadi, ya kirkiro da tsarin cikin kudurorin gwamnatinsa guda 12, wanda hakan ya sanya abokan hadaka da dama suka samar da dauki a cikin tsarin.
Aboan hadakar, sun kasance suna bayar da tallafin kudade, musamman domin a kara habaka noman da manoman Jigawa ke yi.
Koda-yake dai, Jigawa ta kasance tana fuskantar kalubalen sauyin yanayi da zaizayar kasar noma da ambaliyar ruwan sama, amma duk da haka; wannan tsarin ya dan samar da sauki kan wadannan matsaloli.
A hirarsa da manema labarai, Shettima ya nuna jin dadinsa kan sakamako mai kyau da tsarin ya samar a fannin noman jihar.
Kazalika, ya yaba da kokarin da gwamnonin jihohi 36 na kasar nan ke ci gaba da yi na ganin an samar da wadataccen abinci a kasar.
Ya kuma yaba kan samar da wannan tsari, wanda ya sanar da cewa; tsarin zai kara taimakawa wajen kara samar da ayyukan yi da yaki da talauci da kuma kara bunkasa fannin tattalin arzikin kasar.
Shettima ya jinjina kan yadda jihar ta kara habaka noman Alkama, musamman daga hekta 30,000 zuwa sama da hekta 110,000, a cikin shekaru biyu da kuma yadda jihar ke da burin samar da wasu hekta 500,000, nan da shekaru biyar masu zuwa.
Bugu da kari, a karkashin tsarin na Gwamna Namadi, an gyara dubban hektar noma tare da bai wa manoman jihar damar yin nomansu.
Gwamnatin ta kuma gyara sabbin guraren da za a yi noman rani, ciki har da kamar na yankin Lallashi da ke Karamar Hukumar Maigatari.
Ta kuma ayyana ci gaba da bai wa manoma daukin kudaden yin nom ba tare da bata wani lokaci ba, ciki har da noman Shinkafa, domin jawo hankalin wadanda suke a jihar da suka kammala manyan makarantu, domin shiga fannin na yin noma a matsayin samun kudaden shiga, domin samun riba.
Haka zalika, gwamnatin ta samar da kayan aikin noma na zamani kan farashai mai sauki tare da kuma kara daukar malaman gona daga 300 zuwa 2,000, wanda hakan ya kara habaka fannin a jihar.
Bugu da kari, gwamnatin ta kuma kara bunkasa fannin kiwon dabbobi da kiwon kajin gidan gona, inda kuma ta dauki kwararrun likitocin dabbobi 300.
Ta yi hakan ne, bisa hadaka da wani gidan gona na kasar Indiya da nufin samar da abincin dabbobin da na kajin gidan gona ta yadda za a dakile yaduwar cututtuka tsakanin dabbobin da samar da wajen yin kiwo.
Haka zalika, a karkashin tsarin an samar da cibiyoyin zamani shida na bayar da horo a mazabu 30 na jihar.
An kuma horas da daliban da suka kammala manayn makarantu 30 da suka samu takardar sheda a fannin kiwon aikin Injiya a Kasar China tare kuma da horas da wasu.
Sun fara gudanar da gwajin ilimin da suka samo a kasar ne, bayan sun koma Jigawa, inda suka harhada taraktocin noma da sauran kayan aikin noma da gwamnatin Jigawa ta shigo da su.
A yanzu haka, daukacin al’ummar jihar na jiran ganin ranar da za a kaddamar da wadannan dubban kayan aikin noma da za a yi amfani da su a jihar, inda suke da yakinin kayan za su samar da kyakkyawan sauyi ga fannin aikin noma na Jigawa.














