Wata kungiya mai zaman kanta, ta horas da kananan masu kiwon dabbobi 50 a Jihar Filato.
Taron bitar na kwana uku, an shirya shi ne, domin horas da mahalartan dabarun kiwon dabbobi da kuma yadda ake gudanar da hada-hadar kasuwancinsu a zamanance.
- An Bukaci Amurka Da Ta Kauracewa Sanya Wasu Sassa Na Muzgunawa Kasar Sin Cikin Kudurin Dokar Tsaron Kasa
- Yawan Jarin Waje Da Kasar Sin Ta Yi Amfani Da Shi A Watan Nuwamban Bana Ya Karu Da Kaso 26.1%
Kazalika, an shirya horon ne tare da hadaka da Bankin Duniya da kuma shirin bunkasa kiwon dabbobi na Filato (PRES).
A cewar masu shirya haron, a karkashinsa; za a ilimantar da wadanda suka amfana da dabarun tare da kara habaka kudaden shiga a fannin noman ciyar da dabbobinsu daga illolin sauyin yanayi.
Jami’in aikin a Jihar Filato, Mista Emmanuel Nando ya bayyana cewa; shekaru da dama da suka wuce, an yi watsi da fannin na kiwon dabbobi a kasar nan.
Acewarsa, an tara su ne, ba wai kawai don ba su horo ba, har ma da batun koya musu dabarun noman ciyawa, wanda hakan zai sanya a dauki fannin a matsayin na kasuwanci.
Ya kara da cewa, sun samar da kayan zamani ne, domin gudanar da hada-hadar kasuwancin dabbobi da kuma dabarun noman ciyawa, wanda hakan zai bai wa wadanda aka horas damar bunkasa sana’arsu ta kiwo a jihar da kuma a kasa baki-daya.














