Hukumar Haramta Fataucin Mutane ta Kasa (NAPTIP) ta mika mutum 11 da aka tseratar daga hannun masu fataucin mutane ga Hukumar Kananan Hukumomi ta Ringim a Jihar Jigawa.
A yayin bikin mikawar da aka gudanar a Dutse, babban birnin jihar, ranar Lahadi, Kwamandan NAPTIP a jihar, Abdulkadir Turajo, ya bayyana cewa ma’aikatan hukumar ne suka ceto wadannan mutane a Lokoja, Jihar Kogi.
- An Bukaci Amurka Da Ta Kauracewa Sanya Wasu Sassa Na Muzgunawa Kasar Sin Cikin Kudurin Dokar Tsaron Kasa
- Yawan Jarin Waje Da Kasar Sin Ta Yi Amfani Da Shi A Watan Nuwamban Bana Ya Karu Da Kaso 26.1%
Turajo, wanda Shugaban Sashen Ayyuka na Hukumar, Yunusa Mohammed, ya wakilta, ya ce dukkan wadanda aka ceto maza ne masu shekaru tsakanin bakwai zuwa 15, kuma daga kauyuka Tsaba, Kunkurawa da Tsabare a Karamar Hukumar Ringim suke.
Ya ce mika su ya samu tallafi ne daga Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Ci gaban Al’umma ta Jihar Jigawa.
Kwamandan ya yaba wa Hukumar Kananan Hukumomi ta Ringim da Ma’aikatar Kananan Hukumomi na jihar bisa saurin daukar mataki, wanda ya bai wa hukumar damar dawo da wadanda aka ceto cikin gaggawa ga iyalansu.
Turajo ya kuma sake jaddada kudurin hukumar na yaki da fataucin mutane ta hanyar gano, ceto da kuma hada wadanda abin ya shafa da iyalansu a fadin kasar.
A yayin karbar yaran da aka ceto, Shugaban Karamar Hukumar Ringim, Badamasi Garba, ya yaba wa NAPTIP bisa wannan mataki.
Garba, wanda Daraktan Gudanar da Ma’aikata na Hukumar, Idana Isah, ya wakilta, ya yi alkawarin cewa hukumar za ta jajirce wajen ingantaccen dawo da yaran cikin al’umma da kuma gyara rayuwarsu, tare da hana faruwar irin wannan abu a nan gaba.













