Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.
A yau shafin namu zai koya muku yadda za ku hada finkason fulawa mai sauki.
Ga dai Abubuwan da ake tanada:
Fulawa, Sikari Gishiri, Yis, Baikin Fauda.
Ga kuma Yadda ake hadawa:
Za ki samu fulawa kamar gwangwani uku, ki zuba a roba sannan ki zuba sikari kamar babban cokali biyu, sai gishiri rabin karamin cokali sai yis babba cokali daya, sai ki zuba ruwan dumi kofi daya da rabi, ki kwaba shi ki jujjuya shi ko ina ya hade, ki dan bubbuga shi kamar minti uku haka, daga nan sai ki rufe shi ki kai shi rana domin ya tashi.
Sai ki hada miyar da za ki ci da shi, ki samu alayyahu da tattasai da dan tumatur. Idan kina so da taruhu da mai, albasa:
Ki soya manki da albasa, sannan ki zuba kayan miyan wanda dama kin jajjaga su, ki soya sai ki zuba magi, gishiri, kori, sannan ki kawo namanki ki zuba ki jujjuya shi,
Idan suka soyu, bayan sun soyu sai ki kawo alayyahunki wanda dama kin yanka shi kin wanke shi, ki zuba ki ci gaba da juyawa, idan suka hade jikinsu sai ki rufe ki bar shi ya dan yi minti biyar haka kafin nan alayyahun ya dahu. Ita wannan miyar ba’a sa mata ruwa. Sannan kwabun funkason ya tashi, sai ki dakko shi ki zuba baikin fauda ki bubbuga shi saboda iskar ta fita, sai ki dora mai a wuta, wasu suna fadada shi da hannu, wasu kuma suna samun murfin wani abu haka mai fadi su yi da shi ko filet haka su rika zubawa suna fadadawa, sannan su jefa shi a cikin mai, za ki ga ya yi ja shi ne ya soyu, sai ki juya saman shi ma ya soyu haka za ki yi har ki gama.
A ci dadi lafiya.














