Kamar yadda hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afirka CAF ta shirya, za a fara gasar cin kofin kwallon kafa ta nahiyar Afirka karo na 35 a kasar Moroko a ranar 21 ga watan Disamban 2025, kuma za a buga wasan karshe ne ranar 18 ga watan Janairun 2026.
Mai masaukin za ta so ta dauki kofin karo na farko tun 1976, yayin da shi kuma Mohammed Salah zai so manta da abin da ke faruwa a Liberpool ta hanyar taimaka wa kasarsa Masar ta lashe kofin tun bayan hakan da ta yi a 2010.
- An Bukaci Amurka Da Ta Kauracewa Sanya Wasu Sassa Na Muzgunawa Kasar Sin Cikin Kudurin Dokar Tsaron Kasa
- Yawan Jarin Waje Da Kasar Sin Ta Yi Amfani Da Shi A Watan Nuwamban Bana Ya Karu Da Kaso 26.1%
Akwai zakakuran ‘yan wasa da dama da tauraruwarsu za ta haskaka a gasar ta bana wadda manyan ‘yan wasan Afirka daga manyan kasashe daban-daban za su fafata domin samun zakaran wannan shekarar.
Azzedine Ounahi (Moroko)
Dan wasan Real Madrid dan asalin Moroko Brahim Diaz shi ne ya fi jefa kwallaye a wasan neman gurbi, to amma Azzesina Ounahi, wanda shi ne ke kokari wajen raba kwallo a tsakiyar tawagar Moroko shi ne dan wasan da ‘yan Moroko za su so su ga yana taka rawar gani a gasar da za a buga a gaban dubban ‘yan kasar.
Matashin wanda ya samu horo a shahararriyar cibiyar horas da ‘yan wasa ta Sarki Mohammed BI, Ounahi ya daure zaman takaici a kungiyar Marseille bayan tafiya kungiyar sanadiyyar rawar gani da ya taka a gasar kofin duniya ta 2022.
Sai dai bayan komawarsa zuwa kungiyar Girona a Sifaniya cikin watan Agusta, tauraruwarsa ta dawo tana haskawa. Moroko, wadda za ta kara da kasashen Comoros da Mali da kuma Zambia a rukunin (A), suna kuma da kwararrun ‘yan wasa kamar mai tsaron raga Yassine Bonou da dan wasan gaba Youssed En-Nesyri.
Mohamed Amoura (Algeria)MAGES
Dan wasan gaban na Wolfsburg ya jefa kwallo 11 wa kasarsa cikin wasanni takwas tun daga watan Maris, ciki har da kwallo uku rigis da ya zura a ragar Mozambikue. Kuma
wannan bajinta da ya nuna ta sa ya zama zabi na farko a tawagar kasarsa.
Duk da cewa Riyad Mahrez ne ginshiki a tawagar, to amma Amoura ya gina kansa a cikin tawagar. Dole ne kasashen Sudan da Butkina Faso da kuma Ekuatorial Guinea da suke tare a rukunin (E) su yi taka-tsantsan da shi saboda yadda yake sharafi a wannan lokacin.
Bictor Osimhem (Nijeriya)
Kawo yanzu za a iya cewa nasarar Nijeriya kusan za a ce ta ta’allaka ne ga rawar da wannan matashin da ke wasa a kungiyar Galatasaray ke takawa a wannan lokacin musamman yadda yake zura kwallaye a kowanne lokaci.
Tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta samu maki 4 ne kacal a cikin 15 da za ta iya samu lokacin da dan wasan mai shekara 26 ba ya nan, a wasannin neman gurbin zuwa gasar cin kofin duniya.
Osimehn na cikin ginshikan kungiyar a karkashin mai horaswa Eric Chelle, kuma Nijeriya ta kasa lashe wasanta na neman cike gurbi da DR Congo, lokacin da aka cire shi a hutun rabin lokaci.
Kokarin da Osimhen zai yi a zai taimaka matukar gaske idan har Nijeriya na son ta matsa gaba daga matsayi na biyu da ta samu a gasar da aka buga a Ibory Coast zuwa lashe gasar gaba daya. Nijeriya, wadda ta lashe kofin sau uku ta fito a cikin rukunin da ya hada da kasashen Tanzania da Uganda da kuma Tunisia a rukunin (C).
Ibrahim Mbaye (Senegal)
Kowa ya san Sadio Mane ne ginshikin kasar a gasar AFCON ta 2021, yayin da Iliman Ndiaye da Ismaila Sarr suke taka rawar gani a gasar Premier, lamarin da ya sa aka samu ‘yan wasan gaba uku gogaggu.
Tsohon dan wasan tawagar matasa ta kasar Faransa, ya samu shiga tawagar manya ta kungiyar PSG a wannan kaka, inda ya fara a wasan da kungiyarsa ta doke Barcelona a farkon kaka.
Mbaye ya fara buga wa Senegal wasa ne a watan da ya gabata a karawarsu da Brazil, sannan ‘yan kwanaki bayan ya zama dan wasa mafi karancin shekaru a kungiyarsa,inda yana da shekra 17.
Rogers Mato (Uganda)
Tawagar ‘yanwasan Uganda ta dawo AFCON tun daga shekara 2019 lokacin da aka fitar da ita a zagayen ‘yan 16, yanzu kuma suna hankoron kai wa wasan karshe a wannan gasa. Kungiyar da ke karkashin jagorancin Paul Put ta kammala a mataki na biyu a rukuninsu na wasannin neman gurbin gasar cin kofin duniya, a bayan Algeria.
Uganda za ta fuskanci jarrabawa a rukunin (C) inda za ta kara da kasashe kamar Nijeriya da Tunisia.
Reinildo (Mozambikue)
Mozambikue za ta isa Moroko a matsayin kasar da ba ta taba zuwa zagayen kifa daya kwala ba a karo biyar da ta halarci gasar AFCON. Sai dai a karon farko tana alfahari da kasancewar daya daga cikin ‘yan wasan gasar Premier a tawagarsu, bayan da Reinildo ya zamo dan kasar Mozambikue na farko da ya buga wasa a gasar Premier bayan ya koma kungiyar Sunderland daga Atletico Madrid a watan Yuli. Wanda ke wasa ta bangaren hagu, dan wasan mai shekara 31 ya taimaka wa kungiyarsa wajen yin ba-zata














