Jihohin Borno da Kano sun lashe matsayi na gaba ɗaya a bangaren maza da mata a Gasar Karatun Alƙur’ani ta Ƙasa ta 2025 da aka gudanar a jihar Borno. Daraktan Cibiyar Nazarin Musulunci ta Jami’ar Usman Dan Fodio da ke Sakkwato, Farfesa Abubakar Yelwa, ne ya sanar da Musa Ahmed Musa daga Borno a matsayin zakaran maza, yayin da Hafsat Muhammad Sada daga Kano ta lashe matsayi na gaba ɗaya a bangaren mata.
Gasar, wadda ta ɗauki tsawon mako guda kuma ita ce ta 40 a jerin, ta haɗa mahalarta 296 daga jihohi 30, inda suka fafata a rukuni shida na karatun Alƙur’ani. Wannan gagarumar gasa ta jawo manyan malamai, mahaddata da baƙi daga sassa daban-daban na ƙasar.
- Jami’an Hisbah Sun Kama Katon-katon Na Giya A Kano
- Ƴansanda Sun Tsaurara MatakanTsaro A Borno Gabanin Ziyarar Tinubu
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ce nasarar karɓar bakuncin gasar ta 2025 alama ce ta dawowar zaman lafiya a jihar. Ya bayyana cewa gasar ta nuna ƙudurin al’ummar Borno na zaman lafiya, ilimi da neman sani, musamman hikimar Ubangiji da ke cikin Alƙur’ani Mai Girma.
Zulum ya taya zakarun murna tare da yabawa duk mahalarta, yana mai cewa nasarar ba wai cin kofi kawai ba ce, illa sakamakon jajircewa, ladabi da girmama Kalmar Allah. Ya ƙara da cewa dukkan matasa maza da mata da suka halarci gasar su ma zakaru ne saboda jajircewarsu wajen neman ilimi da shiga wannan gasa mai albarka.
Gwamnan ya kuma nuna godiya ga Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da uwargidansa Hajiya Nana Kashim Shettima, gwamnonin jihohi da mataimakansu, sarakunan gargajiya, Jami’ar Usman Dan Fodio da sauran manyan baƙi. Taron ya samu halartar uwargidan Mataimakin Shugaban Ƙasa, Gwamnan Katsina Dikko Umaru Radda, Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi, ’yan majalisa, malamai da sauran fitattun jama’a.














