Tun bayan da gwamnatin Tinubu ta karɓi ragamar mulkin Nijeriya, wani abu baƙo da ke shirin zama ruwan dare, kullum kamar ƙara yawaita yake yi, wannan abu ba komai ne fa ce mu ce “U-turn”, a turance, ma’ana “naɗa muƙamai da soke su”.
U-turn a cikin naɗe-naɗen gwamnati yana nufin lokacin da shugaban ƙasa ya fara sanar da naɗin muƙami sannan daga baya ya janye naɗin, ko ya maye gurbin wanda aka naɗa, ko soke naɗin gaba ɗaya.
Duk da cewa, gwamnatin tana da mafakarta kan hakan, amma da yawa suna tambaya, meke hana a duba duka abubuwan da suka dace kafin sanar da naɗin ga jama’a?
Amma kafin muji amsar wannan daga gwamnati, bari mu fara duba hasashen manyan dalilan da ka iya janyo gwamnati ta janye naɗin muƙami bayan ta sanar da naɗin a bainar jama’a.
1. Ƙorafin Jama’a da Siyasa
Sau da yawa akan janye naɗe-naɗe bayan suka mai ƙarfi daga jama’a, ko masu ruwa da tsaki, ko ƙungiyoyin siyasa. Misali, an janye naɗin wani matashi mai shekaru 24 a matsayin shugaban FERMA bayan suka da aka yi masa cewa ba shi da ƙwarewar da ake buƙata, wanda hakan ya sanya shugaban ƙasa ya janye naɗin.
Hakazalika, akwai wani jerin sunayen wasu manyan mutane da aka yi yunƙurin naɗawa a matsayin jakadu, bayan shan suka a kafafen sada zumunta, dole hakan ya haifar da matsin lamba ga gwamnati ta janye sunayen don sake duba lamarin.
2. Matsin lamba daga ‘ya’yan Jam’iyyar Cikin Gida (mai mulki) ko daga masu ruwa da tsaki
Wani lokaci, janye naɗin na zuwa ne bayan ƙorafe-ƙorafen cikin gida ko ƙorafe-ƙorafe masu tasiri daga masu ruwa da tsaki da suka buƙaci sauye-sauye – misali, tutsun ‘ya’yan jam’iyyar APC ko masu ruwa da tsaki na jiha kan waɗanda aka naɗa a muƙamai.
A cikin sake fasalin kwamitin Hukumar Neja-delta (NDDC), an canza waɗanda aka naɗa na asali bayan tutsun da magoya bayan jam’iyyar APC na yankin suka yi.
3 – Rashin Jituwa da Haɗin kai a tsakanin manyan ofisoshin gwamnati wajen yanke shawara
Masu sharhi kan al’amuran dake faruwa a ƙasa, sun bayyana rashin daidaiton haɗin kai a cikin fadar shugaban ƙasa a matsayin abin da ke haifar da hakan, inda ake fitar da sanarwar naɗin muƙami kafin a kammala duk wani bincike da bayanai, wanda ke haifar da jin kunya na yin amai a lashe a babbar Fada irin ta shugaban ƙasa.
Wannan yana nuna cewa, wani lokacin ana sanar da yanke shawara kafin a samu cikakken amincewa daga sauran ofisoshin gwamnati.
5. Dabarun Siyasa
Wasu sauye-sauyen na iya faruwa ne sakamakon dabarun siyasa, kamar daidaita muradun yanki, kwantar da hankalin masu suka, ko hana rarrabuwar kawuna a cikin jam’iyya mai mulki.
Wannan dambarwar na nuna cewa, ra’ayin jama’a da na masu ruwa da tsaki, da tsarin jam’iyya mai mulki, da kuma dabarun siyasa na taka muhimmiyar rawa wajen naɗe-naɗe da sauye-sauyen muƙamai ko da bayan an fitar da sanarwar ne.
Ga wasu daga cikin jerin naɗe-naɗe da sauye-sauyen muƙamai a gwamnatin Shugaba Tinubu.
Shugaban NERC – Abdullahi Ramat
Shugaba Tinubu ya soke naɗin Abdullahi Ramat a matsayin Shugaban NERC inda ya maye gurbinsa da Oseni.
Zaɓaɓɓun Ministoci – Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasir elrufa’i da Maryam Shetty
Duka su biyun an aika da sunan su don tantancewa a Majalisar Dattawa a matsayin waɗanda aka zaɓo a matsayin ministoci amma an janye sunansu inda kuma aka maye gurbinsu da wasu.
Karamin Ministan Ma’aikatar Gidaje da Raya Birane – Abdullahi Tijjani Muhammmad Gwarzo
Bayan majalisar dattawa ta tantance Gwarzo a matsayin karamin Minista da zai yi aiki tare da Babban Minista Ahmed Musa Dangiwa amma watan Agustan 2023 amma a watan Oktoban 2024 aka sauke shi daga muƙaminsa.
Shugabannin NTA
Shugaba Tinubu ya naɗa sabbin shugabanin gudanarwar gidan Talabijin na Nijeriya (NTA) – ciki har da Rotimi Pedro a matsayin DG da sauran manyan jami’ai, amma daga baya aka soke sabbin naɗin, inda ya mayar da Salihu Abdullahi Dembos a matsayin DG da Ayo Adewuyi a matsayin Babban Daraktan Labarai.
Shugaban Hukumar UBEC — Idris Olorunnimbe
An naɗa Olorunnimbe a matsayin Shugaban Hukumar Ilimi Ta Bai-ɗaya (UBEC) amma daga baya aka soke naɗin, aka maye gurbinsa da Tanko Umaru Al-Makura.
Taƙaddamar Naɗin Jakadu.
Bayan bayyanar sunayen wasu fitattun mutane a cikin jerin sunayen jakadun da aka yi yunƙurin naɗawa, taƙaddama ta kaure inda ta haifar da janye sunayen wasu daga ciki.
Muheeba Dankaka — Hukumar Halayyar Tarayya (FCC).
An sake naɗa ta a wa’adi na biyu na shekaru biyar-biyar a matsayin Shugabar FCC amma an janye naɗin bayan sa’o’i kaɗan, an maye gurbinta da Ayo Omidiran.
Zaɓaɓɓun Kwamishinonin Zaɓe na INEC (REC)
An sauya zaɓen Mohammed Ngoshe (Borno) da Owede Kosioma Eli (Bayelsa), inda aka maye gurbinsu da wasu.
Shugaban FERMA — Kashim Imam
An sanar da Kashim Imam a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Hanyoyin Tarayya (FERMA) amma an janye naɗin cikin ‘yan kwanaki saboda cece-kuce game da ƙwarewa da shekarunsa.
Ruby Onwudiwe — kwamitin gudanarwar Daraktocin CBN
An zaɓe ta a matsayin mamba na kwamitin gudanarwa na Babban Bankin Nijeriya (CBN). An janye zaɓen bayan takaddamar siyasa game da jam’iyyarta.
Hukumar Raya Yankin Neja Delta, (NDDC)
An naɗa Asi Okang (Kuros Riba) da Victor Akinjo (Ondo) da farko a kwamitin NDDC amma an maye gurbinsu duka cikin sa’o’i 24 bayan tutsun da ‘ya’yan Jam’iyyar APC na yankin suka yi.
A irin wannan halin, ba a jima ba, fadar shugaban kasa, ta yi afuwa ga Maryam Sanda wacce ta kashe Mijinta, kuma kotu ta yanke mata hukuncin kisa amma da jama’a suka fara ƙorafi sai aka janye afuwar.













