Birnin Oyo a jihar Oyo ya cika da farin ciki a ranar Lahadi, yayin da manyan jami’an gwamnati, da magoya baya da sarakunan gargajiya suka hallara domin bikin naɗa sababbin sarakunan gargajiya da Alaafin na Oyo, Oba Abimbola Owoade I, ya jagoranta a fadarsa.
A yayin bikin, Barrista Seyi Tinubu, ɗan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya samu naɗin sarautar “Okanlomo na Yorubaland”, wato ɗan da Yorubawa ke ƙauna. Haka kuma, Sanatan Zamfara ta Yamma kuma tsohon Gwamnan Zamfara, Abdul’Aziz Yari, an tsara naɗa shi a matsayin “Obaloyin na Yorubaland” a wannan biki.
- Gamayyar kungiyoyin Seyi Tinubu (STSG) Na Shirin Gangamin Taronta Na Kasa
- Borno Da Kano Sun Zama Zakaru A Gasar Karatun Alƙur’ani Ta Ƙasa Ta 2025
Bikin ya samu halartar Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, tare da Sanatoci da dama ciki har da Jagoran Majalisar Dattawa Opeyemi Bamidele da Sanatan Lagos ta Gabas, Mikhail Tokunbo. Haka kuma, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Oyo, Hon. Adebo Ogundoyin, da tsohon Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, na daga cikin manyan baƙin da suka halarta.
Bayan bikin, Ogundoyin ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa yana matuƙar farin ciki da girmamawa da aka yi wa Seyi Tinubu a fadar Alaafin. Ya bayyana bikin a matsayin wata babbar alama ta al’adu, da tarihi da shugabanci, yana mai cewa jajircewar Seyi Tinubu wajen bunƙasa matasa, da tallafawa ƙirƙire-ƙirƙire da haɗin kan ƙasa na ci gaba da zaburar da jama’a.
Ya ƙara da cewa wannan sarauta ba wai girmama asalinsa na ɗan Shugaban Ƙasa kaɗai ba ce, illa shaida ce kan tasirin da Seyi Tinubu ke da shi a rayuwar jama’a da kuma rawar da yake takawa wajen haɗa yanki daban-daban a Nijeriya.













